Daga Fita gefen Gari, Ƴan Mata 20 Sun Gamu da Ƴan Bindiga Ɗauke da Bindigogi a Zamfara
- Ƴan bindiga sun yi awon gaba da mata 20, mafi yawancinsu ƴan mata a garin Moriki da ke ƙaramar hukumar Zurmi a Zamfara
- Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun tattara matan ne a lokacin da suka fita wajen gari domin samo itacen girki
- Har kawo yanzu babu wata sanarwa daga rundunar ƴan sandan jihar Zamfara kan wannan sabon hari da ya auku a yankin Zurmi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mata akalla 20 a wani sabon samame da suka kai yankin ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Rahotanni daga yankin sun nuna cewa ƴan ta'addan sun sace matan, waɗanda yawancinsu ƴan mata ne masu karancin shekara a kauyen Moriki.

Source: Original
Ƴan bindiga sun sace mata 20 a Zamfara
Wani mazaunin garin Moriki mai suna Sufyanu Moriki ya shaida wa Channels tv cewa an sace matan ne a lokacin da suka fita samo itacen girki a dajin gefen gari.

Kara karanta wannan
An tsinci gawar wata budurwa a kusa da Masallaci, ƴan sanda sun ga alamu 2 a wurin
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“An yi garkuwa da su ne a ranar Asabar da ta gabata, sun fita samo itacen girki a dajin wajen garin lokacin da ‘yan bindigar suka kai musu hari, suka tafi da su."
“Har yanzu ba su kira ko suka tuntubi kowa don neman kudin fansa ba," in ji shi.
Har kawo yanzu rundunar ‘yan sanda reshen jihar Zamfara ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba tukuna.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya bayyana cewa bai samu rahoton lamarin ba, kuma ya yi alƙawarin zai fitar da bayani idan ya samu cikakken rahoto.
Asalin abin da ya kawo matsalar tsaro a Arewa
Ana ganin dai matsalar ‘yan bindiga ta samo asali ne daga rikicin filaye da wurin kiwo tsakanin makiyaya da manoma a Arewacin Najeriya.
Sai dai a yanzu rikicin ya rikide zuwa laifuffukan da ke da nasaba da gungun miyagu, inda suke addabar al’ummomin karkara da ba su da isasshen kariya ko wakilci daga gwamnati.
Wannan lamari na kara tsananta matsalar yunwa da rashin abinci mai gina jiki a yankin Arewa maso yamma, sakamakon yadda hare-haren ke tilasta wa mutane barin gonakinsu.

Source: Facebook
A watan da ya gabata, 'yan bindiga a Zamfara sun kashe mutane 33 da suka sace tun watan Fabrairu, duk da sun karɓi kuɗin fansa da ya kai $33,700.
Haka nan, ana cewa jarirai uku sun mutu a hannun masu garkuwa da mutane, kamar yadda jami'ai da mazauna yankin suka shaida wa manema labarai.
Sabon harin Moriki da aka yi garkuwa da ƴan mata ya ƙara nuna halin da wasu yankuna ke ciki na rashin tsaro a Zamfara, rahoton Daily Post.
Yan bindiga sun kai hari a yankin Birnin Magaji
A wani rahoton, kun ji cewa ƴan bindiga sun sace mutane a lokacin da suka kai hari yankin ƙaramar hukumar Birnin Magaji a Zamfara.
Miyagun 'yan bindigan sun sace mutane biyar tare da sace shanu guda huɗu a safiyar ranar Lahadi da misalin ƙarfe 9:00 na safe a kauyen Kasheshi Kura.
Wannan mummunan harin na 'yan bindiga ya jefa mazauna garin cikin fargaba da rashin tabbas dangane da tsaron rayuka da dukiyoyinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
