Dakarun Sojoji Sun Toshe Kofofin Tsira ga 'Yan Boko Haram da ISWAP, an Kashe Miyagu
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarori kan 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP a jihohin Borno da Adamawa
- Jami'an tsaron sun hallaka 'yan ta'adda masu yawa a hare-haren da suka kai musu a maboyarsu da ke cikin daji
- Sojojin sun kuma samu nasarar kwato makamai da dama da sauran kayayyaki daga wajen miyagun 'yan ta'addan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Dakarun sojoji karkashin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), sun kashe mayakan Boko Haram/ISWAP 17 yayin wasu hare-hare.
Dakarun sojojin sun samu nasarar kashe 'yan ta'addan ne a jihohin Borno da Adamawa.

Source: Twitter
Mukaddashin daraktan watsa labarai na rundunar sojoji, Kyaftin Reuben Kovangiya, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun samu nasara kan 'yan Boko Haram
Ya ce mayakan na Boko Haram/ISWAP suna aiki a yankunan Bama, Konduga, Gwoza, Magumeri da Biu a jihar Borno, da kuma Michika a jihar Adamawa inji rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Mukaddashin daraktan ya ce dakarun wadanda suka jajirce sun kuma gano tare da tarwatsa abubuwan fashewa fiye da guda 14 da 'yan ta’addan suka dasa a wurare daban-daban ba tare da asarar rai ba.
"A kokarin ci gaba da hana 'yan Boko Haram/ISWAP damar sararawa, dakarun OPHK, tare da goyon bayan jiragen yakin rundunar sama da kuma hadin gwiwar 'yan sa-kai, sun gudanar da jerin hare-hare a yankin Arewa Maso Gabas daga 23 ga Yuli zuwa 2 ga Agusta, 2025."
"Wannan ya haɗa da sintiri da farmaki, kwanton-bauna, share maboyar 'yan ta’adda da kuma dakile hanyoyin samun kayan abinci da makamansu, a yankunan Michika na Adamawa da kuma kananan hukumomin Bama, Konduga, Gwoza, Magumeri da Biu na jihar Borno."
"Hare-haren sun kai ga hallaka 'yan ta’adda da dama, kwato makamai da harsasai masu tarin yawa, da kuma tarwatsa bama-bamai cikin nasara tare da kwace kayan abinci da na yau da kullum mallakin 'yan ta’addan."
- Kyaftin Reuben Kovagiya

Source: Twitter
Jami'an Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda
Reuben Kovangiya ya ƙara da cewa a wasu hare-hare daban a yankunan Bula Daburu, Alau Dam, Bitta, Kawuri, Algambari, Ajiri da Bulabulin, sojoji sun kashe sama da 'yan ta’adda 17 na Boko Haram/ISWAP tare da kwato bindigogi AK-47 da dama, bindigar PKT da harsasai.
Ya kuma bayyana cewa a cikin wannan lokacin, sojojin sun taimaka wajen dawo da sama da mutane 987 da suka tsere sakamakon rikicin, zuwa garuruwansu na asali a Mandaragrau, karamar hukumar Biu ta jihar Borno.
'Yan sanda sun hallaka 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara sun samu nasara kan 'yan bindiga yayin wani artabu da suka yi.
Jami'an yan sandan tare da hadin gwiwar 'yan sa-kai sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga guda takwas bayan an yi kazamin musayar wuta.
An dai fafata ne bayan da 'yan bindiga suka yi wa jami'an tsaron kwanton bauna a kan hanyarsu ta zuwa kai daukin gaggawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
