Gwamnatin Tinubu Ta Kara Martani ga Su Kwankwaso kan Zargin Nuna Wariya ga Arewa
- Gwamnatin tarayya ta ce fiye da rabin kasafin ayyuka na 2024 da 2025 an ware su ne don yankin Arewa don ci gaban yankin
- Darakta Janar a ofishin kasafin kudi na kasa, Tanimu Yakubu ya karyata zargin wariya da wasu fitattun ’yan Arewa
- Manyan 'yan siyasar shiyyar kamar su Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Babachir Lawal sun zargi gwamnati da watsi da Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Tanimu Yakubu, Darakta-Janar na ofishin kasafin kuɗi na tarayya, ya karyata cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi watsi da Arewa ta fuskar manyan ayyuka.
Ya ce fiye da rabin kasafin kuɗi na manyan ayyukan ci gaba na shekaru 2024 da 2025, an ware su ne domin ayyuka a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan
Talaka bawan Allah: ADC ta fusata da Tinubu zai kashe N712bn a gyaran filin jirgin Legas

Source: Facebook
The Cable ta wallafa cewa wannan bayani na zuwa ne bayan zarge-zargen tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal kan watsi da yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shi ma shugaban kwamitin amintattu na kungiyar dattawan Arewa (ACF), Bashir Dalhatu ya yi zargin gwamnatin na nuna wariya ga yankinsu.
'Ana ayyuka a Arewa,' Gwamnatin Tinubu
Daily Post ta wallafa cewa a martaninsa, Yakubu ya ce irin wannan zargi na wariya ba shi da tushe domin gwamnatin Tinubu na gudanar da tsare-tsare masu ma’ana ga yankunan kasar nan.

Source: Facebook
A cewarsa, Arewa ce ke kan gaba a jerin wuraren da gwamnatin tarayya ke mayar da hankali wajen kashe kudi, inda ta samu fiye da rabin kasafin kuɗi na ayyuka a 2024 da 2025.
Yakubu ya ce gwamnati na aiwatar da ayyuka kamar hanyar Abuja–Kano, babbar hanyar Sokoto–Badagry mai kuɗin Naira tiriliyan 12.1.
Ayyukan gwamnatin Bola Tinubu a Arewa
Ya kara da cewa akwai babban aikin titi mai tsawon kilomita 1,068 da ake shirin yi, inda aka amince da kashe Naira tiriliyan 3.63 domin aiwatar da matakan farko a jihohin Sokoto da Kebbi.
Haka kuma, akwai aikin layin dogo na Kano zuwa Maradi, layin wutar lantarki daga Zungeru zuwa Kano, da kuma faɗaɗa filayen jiragen sama a Katsina, Maiduguri da Kaduna.
Ya ƙara da cewa ana gina tashoshin ajiya da fitar da kayan noma na tsandauri a Funtua da Bauchi don bunkasa kasuwancin amfanin gona.
Baya ga haka, gwamnatin na zuba jari a aikin kula da albarkatun ruwa da noman rani, musamman a yankunan Sokoto-Rima da Binuwai.
Ya kuma bugi kirji a kan cewa ana ƙarfafa matakan tsaro a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya ta hanyar ƙarin kuɗin da aka ware wa rundunonin tsaro.
Hadimin Ganduje ya caccaki salon mulkin Tinubu
A wani labarin, mun wallafa cewa hadimin tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda Bola Tinubu ke tafiyar da mulkinsa.
Tun bayan murabus ɗin Ganduje daga shugabancin APC, Salihu, da aka fi sani da Dawisu ya fara fitowa yana cewa abubuwa da dama ba sa tafiya yadda ya kamata a gwamnatin.
Yakasai ya zargi shugaban ƙasa da sauya salon mulkinsa zuwa wanda ba ya amfani wasu yankuna, ciki har da jihar Kano, amma an fifita jihohi kamarsu Legas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
