Za a Sheka Ruwan Sama a Kano, Kaduna, NiMET Ta Hango Ambaliya a Jihohi 3
- Hukumar NIMET ta ce za a samu ruwan sama da tsawa a jihohin Arewa kamar Adamawa, Taraba, Jigawa da Bauchi a safiyar Talata
 - Da yamma kuma, za a yi ruwan sama a Gombe, Zamfara, Borno, Kaduna da Kano, wanda zai iya daukar lokaci mai tsawo
 - NIMET ta yi gargadin ambaliya na iya faruwa a Bauchi, Kaduna da Plateau, ta bukaci jama’a su dauki matakan kariya
 
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Hukumar hasashen yanayi a Najeriya, NIMET ta yi bayani kan hasashen yau Talata a Najeriya.
Hukumar NIMET ta ce za a sheka ruwan sama a wasu jihohin Arewa da ta ce akwai fargabar samun ambaliyar ruwa.

Source: UGC
Ruwan sama: Hasashen NIMET a yau Talata
Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a daren jiya Litinin 4 ga watan Agustan 2025 a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NIMET ta ce da safiyar yau Talata 5 ga watan Agustan 2025 za a samu tsawa da ruwan sama matsakaici a Adamawa.
Sauran jihohin da hukumar da jero sun hada da Taraba, Bauchi, Jigawa, Kano da kuma jihar Kaduna da ke Arewa maso Yamma.
Fargabar samun ambaliya a wasu jihohi
Har ila yau, Hukumar ta ce a yammacin yau Talata za a samu matsakaicin ruwan sama da kuma tsawa a wasu jihohin Arewacin Najeriya.
Jihohin sun hada da Gombe, Bauchi, Zamfara Kaduna, Kano da kuma Borno wanda zai dauki wani lokaci.
Sai dai kuma hukumar ta yi gargadin za a iya samun ambaliyar ruwa a jihohin Bauchi da Kaduna da kuma Plateau.

Source: Original
Hasashen ruwan sama a Abuja da Nasarawa
Bugu da kari, NIMET ta bayyana a yankin Area ta Tsakiyar Najeriya, za a samu matsakaicin ruwa a jihohin Niger da Kogi.
Sannan birnin Abuja zai samu ruwa, sai kuma Nasarawa da Kwara da Plateau da kuma jihar Niger.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Adamawa da jihohi 7 za su fuskanci ambaliya daga Litinin zuwa Laraba
Wannan hasashen ya biyo bayan shiga watan Agusta da ake yawan samun ruwa a kai a kai ba tare da kakkautawa ba.
Hukumar NiMET ta ce da safiyar Talata za a samu ruwa a jihohin Kudancin Najeriya da suka hada da Enugu da Edo.
Sauran sun hada da Ondo da Anambra da Cross Rivers, Rivers da kuma jihar Delta a Kudu maso Kudancin kasar.
Sai dai hukumar ta ce za a iya fuskantar ambaliya a jihohin Lagos, Oyo, Ogun, Akwa Ibom, Bayelsa.
Sai kuma jihohin Cross River da Delta inda ta shawarci alumma da su dauki matakan kariya kan abin da ka iya biyo baya.
NiMET ta fitar da hasashen wata Agusta
Kun ji cewa hukumar NiMet ta bayyana cewa ruwan sama da ya wuce kima zai sauka a jihohin Arewa 10 da suka hada da Sokoto, Zamfara a watan Agusta.
Hukumar ta ce za a samu saukin ruwa a Arewa ta Tsakiya, NiMet ta ce akwai yiwuwar jihohin Kudu maso Yamma su fuskanci fari.
Ta ba jama’a shawara da hukumomi da su shirya don tunkarar ambaliya, cututtuka da sauran abubuwan da ruwan Agusta zai zo da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
    