Nafisa: Pantami Ya Nemi Tinubu Ya Karrama 'Yar Yobe da Ta Ci Gasar Turanci a Duniya
- Sheikh Isa Pantami ya nemi a ba Nafisa kyautar $100,000, gida da lambar OON bisa bajintarta a gasar TeenEagle
- Nafisa Abdullah Aminu ta doke ‘yan takara sama da 20,000 daga kasashe 69 a fagen harshen Turanci
- Pantami ya ce malaminta ma ya cancanci lada kamar yadda ake yi wa masu horar da ‘yan wasan kwallon Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Tsohon ministan sadarwa Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya bayyana cewa ya kamata a karrama Nafisa Abdullah Aminu.
Nafisa ce ɗalibar da ta lashe gasar TeenEagle ta duniya a fannin harshen Turanci, kuma a kan haka ne Pantami ya ce ta cancanci kyauta daga gwamnatin tarayya.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanin da Sheikh Isa Ali Pantami ya yi ne a cikin wani sako ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Daliba daga Yobe ta yi bajinta, ta yi fata fata da ƙasashen Turawa 69 a gasar Turanci
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce nasararta ba abin alfahari ba ce kawai ga Yobe da Najeriya gaba ɗaya, hakan shaida ce cewa ‘yan Najeriya matasa na da hazaka matuƙa idan aka ba su dama.
Sheikh Pantami ya ce irin wannan nasara ta cancanci irin lambar yabo da aka bai wa ‘yan wasan Najeriya mata.
Nafisa ta yi nasara bayan doke kasashe 69
Sheikh Pantami ya bayyana cewa Nafisa mai shekara 17 daga Yobe ta doke sama da ‘yan takara 20,000 daga kasashe 69 a gasar TeenEagle da aka gudanar a London.
Ya ce wannan nasara ta tabbatar da cewa hazaka ba ta da iyaka, kuma Najeriya na da dimbin matasa da za su iya wakiltar ƙasar da kyau a matakin duniya.
“Saboda wannan gagarumar nasarar, akwai bukatar a yi mata tarba da yabo na musamman daga gwamnatin tarayya,”
- In ji Pantami.
An nemi karrama Nafisa da malaminta

Kara karanta wannan
Talaka bawan Allah: ADC ta fusata da Tinubu zai kashe N712bn a gyaran filin jirgin Legas
Sheikh Pantami ya ce kamar yadda ‘yan kwallon mata na Najeriya suka samu kyautar $100,000 da gida mai dakuna uku da kuma lambar yabo ta OON, ita ma Nafisa ta cancanci haka.
Ya kuma ce malaminta na harshen Turanci ya cancanci a ba shi lada, kamar yadda aka bai wa masu horas da ‘yan kwallon Najeriya.

Source: Facebook
'Ilmi ne matakin gina ƙasa' - Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa ba za a samu ci gaban ƙasa ba sai da bunƙasa harkar ilimi.
Ya ce gwamnati da al’umma su daina yi wa ilimi kallon hadirn kaji, domin ba za a samu cigaba ba sai da gina matasa da malamai.
A ƙarshe, Sheikh Pantami ya yi kira da a gayyaci Nafisa da malaminta zuwa fadar shugaban ƙasa domin a karrama su.
A cewar shi:
“Ina kira da a gayyato ‘yar mu, wadda ta zama abin alfahari ga kowa da kowa a Najeriya."
Tinubu ya karrama 'yan wasan Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta karrama 'yan wasan Najeriya da suka wakilci kasar a gasar kwando.
'Yan wasan D'Tigress mata da suka wakilci Najeriya sun yi nasarar lashe kofi kamar yadda 'yan Super Falcons suka yi.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da basu makudan kudi har $100,000 da gidaje a birnin tarayya Abuja da lambar girmamawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng