'Sau 3 Muna Zama da Turji a Wata 1': Shehin Malami Ya Ja Hankalin Hukumomi kan Sulhu
- Musa Yusuf Assadus Sunnah ya sake bayyana damuwarsa kan ta'addanci, yana cewa matsalar Arewa maso Yamma ta yi tsanani fiye da yadda ake tsammani
- Ya ce sun ziyarci Bello Turji sau uku a watan da ya wuce domin zaman sulhu, inda suka fuskanci haɗari don ceto al’umma daga bala’i
- Malamin ya koka kan yadda wasu ke sukar kokarinsu, duk da suna shiga hatsari suna wa'azi da rokon 'yan bindiga da su ji tsoron Allah
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya sake yin magana kan ta'addanci da ke faruwa musamman a Arewa maso Yamma.
Sheikh Assadus Sunnah ya ce tabbas akwai matsala musamman game da abubuwan da suke gani.

Source: Facebook
Sheikh Assadus Sunnah ya sake magana kan ta'addanci
Malamin ya bayyana haka a cikin wani bidiyo yayin karatu na musamman kan tsaro a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, malamin ya ce idan har ya bayyana irin karfin da yan bindiga suke da shi mutane za su yi mamaki.
Ya kara jaddada muhimmancin sulhu da yan bindiga duba da abin da ke faruwa musamman ma rasa rayuka.
Ya ce:
"Alhamdulillahi muka tashi muka tafi karkashin wannan kwamitin domin zaman sulhu.
"Da yawa idan na ce na je na gano Turji ido da ido mamaki ma yake, a cikin watan nan da ya wuce sau uku muna zuwa.
"Kamar yadda muke zaune da kai haka, ta ganin Annabin tsohuwa kuru-kuru gani ga shi yana gani na ina ganinsa.
"Kuma mun tashi a gabansa mun fada masa a ji tsoron Allah akwai abubuwan da ake yi wadanda ba daidai ba ne."

Source: Facebook
Abin da Assadus Sunnah suka fadawa Bello Turji
Sheikh Musa Assadus Sunnah ya ce a matsayinsu na malamai sun fadawa Bello Turji da sauran yan uwansa gaskiya kan abin da ke faruwa.

Kara karanta wannan
Shugaban Iran ya gargaɗi Tinubu kan tsoma baki a rikici da Isra'ila? An samu bayanai
Ya ce sun yi musu wa'azi kan cewa su ji tsoron Allah kan abubuwan da suke yi saboda akwai kura-kurai a ciki.
Ya kara da cewa:
"Sun yi magana,'mun yi magana, sun fadi dalilansu, duk wanda ya ke ji shi namiji ne ya zo mu dauke shi ya je can a gabansu ya ce musu su ji tsoron Allah."
Malamin ya bayyana hatsarin da suka shiga duk domin ceto al'umma daga bala'in da ta shiga amma wasu na sukarsu.
Shehin ya koka kan wasu da ke zaune a cikin gari ba su san komai ba sai dai su dura muku zagi yayin da kuke ƙoƙarin ceto al'umma.
Turji: Shinkafi ya magantu kan matsalar tsaro
Kun ji cewa mai sharhi kan matsalar tsaro, Sani Shinkafi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dakile rundunar CJTF da CPG daga kashe Bello Turji a Zamfara.
Shinkafi ya ce CJTF da CPG na dab da shafe babin Turji, gwamnatin tarayya ta ce su koma Shinkafi.
A cewarsa, gwamnatin tarayyar ta ce za ta yi sulhu da shugaban ƴan ta'addar, abin da Bello Turji ya ƙi amincewa da shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
