Kaduna: Gwamna Ya Faɗi Rashin Ɗa'a da Ƴan Siyasa Ke Yi Wa Malaman Addini

Kaduna: Gwamna Ya Faɗi Rashin Ɗa'a da Ƴan Siyasa Ke Yi Wa Malaman Addini

  • Gwamna Uba Sani ya yaba da rawar da shugabannin addini da na gargajiya ke takawa wajen samar da zaman lafiya a Kaduna
  • Sanata Uba Sani ya ce nasarar "Kaduna Peace Model" ta bulla ne bisa hadin kai da shugabannin addini, al’umma da jami’an tsaro
  • Shugaban CAN na Arewa, Rabaran John Hayab, ya ce gwamnatin Uba Sani na kawo sauyi ta hanyar jagoranci da ya hada kowa da kowa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Gwamna Uba Sani na Kaduna ya yaba da muhimmancin malaman addini a zaman lafiyar jihar.

Uba Sani ya danganta zaman lafiyar da ake samu a jihar da kokarin shugabannin addini da na gargajiya masu hada kan jama’a.

Gwamna ya jaddada muhimmancin malamai a zaman lafiya
Gwamna Uba Sani ya bayyana amfanin malaman addini a zaman lafiya. Hoto: Uba Sani.
Source: Facebook

Uba Sani ya fadi muhimmancin malaman addini

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da shugabannin addini da na gargajiya a Kaduna, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Sukar Tinubu: El Rufai ya debo ruwan dafa kansa, APC ta yiasa martani mai zafi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai girma Gwamna Uba Sani ya ce ba za a samu zaman lafiya ba sai da taimakonsu wanda ya yi tasiri matuka.

Ya ce:

“Da ba don shugabannin addini ba, da ba za mu tsaya nan muna murnar zaman lafiya ba. Sune suka fara ba ni shawara tun farko."

Taron ya gudana ne karkashin kwamitin zaman lafiya da hadin kan addinai na Kaduna, a cikin bikin cika shekaru biyu da mulkinsa.

An shirya taron ne ta hannun Hukumar Kula da Addinai ta Jihar Kaduna don karfafa zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’umma.

Gwamna Uba Sani ya soki ‘yan siyasa da ke zuwa wurin malamai da addini ne kawai idan zabe ya karaso domin neman goyon baya.

Ya kara da cewa:

"Muna zuwa wurin malamai ne da zarar zabe na karatowa, mu nemi su mara mana baya ta fuskar addini. Wannan ba daidai ba ne."
Uba Sani ya fadi muhimmancin malaman addini a Kaduna
Gwamna Uba Sani ya shawarci yan siyasa kan mu'amala da malamai. Hoto: Uba Sani.
Source: Facebook

Kaduna: Bukatar Uba Sani ga malaman addini

Kara karanta wannan

Abincin wasu ya ƙare: Bayan ambaliya, Gwamna Zulum ya kori wasu kwamishinoni

Ya ce malamai suna da muhimmanci wajen shugabanci ba wai a lokacin zabe kadai ba, ya bukaci su rika rike gwamnati da gaskiya da rikon amana.

A cewarsa, nasarar tsarin zaman lafiya na Kaduna ya ta’allaka da shawara, fahimta da hadin kai tsakanin kabilu da kungiyoyin addini.

“Jihar Kaduna ta kirkiri tsarin zaman lafiya na hanyar fahimta da sulhu. Yanzu wasu jihohi suna kwaikwayonmu.”

- Cewar Uba Sani

Ya bayyana cewa gwamnati ta yi amfani da hanyoyin sulhu ba tare da amfani da karfi na jami’an tsaro ba sai an fara tuntubar jama’a.

Gwamnan ya jaddada cewa da hadin kai ne aka samu sauki a Birnin Gwari wanda a da ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda, TheCable ta ruwaito.

Ya soki ‘yan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta wajen bata sunan malamai domin samun karfin siyasa ko daukaka.

Ya ce:

“Idan muka bar a ci mutuncin shugabannin addini, ba za mu iya gina kasa ba, balle jiha. Wannan abu ne mai hatsari.”

Ya roki malamai su ci gaba da zama masu fadar gaskiya ga al’umma, tare da alkawarin ci gaba da kare su daga cin zarafi.

Kara karanta wannan

Tinubu: Za a fara daukar sunayen manoman gaskiya domin raba musu tallafi

Taron ya samu halartar jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, malamai na addinai biyu, jami’an tsaro da kungiyoyin farar hula.

Uba Sani ya yi garambawul a gwamnatinsa

Kun ji cewa Gwamna Uba Sani ya sauya mukaman kwamishinan shari’a da na tsaro da harkokin cikin gida domin inganta ayyuka.

Yayin da aka dage Sule Shuaibu daga ma’aikatar shari'a zuwa ta tsaron cikin gida, James Kanyip ya zama sabon babban lauyan jiha.

Uba Sani ya bukaci kwamishinonin su zage damtse wajen kawo sauyi a yaki da ‘yan bindiga da gyaran shari’a a jihar Kaduna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.