An Tsinci Gawar Wata Budurwa a Kusa da Masallaci, Ƴan Sanda Sun Ga Alamu 2 a Wurin

An Tsinci Gawar Wata Budurwa a Kusa da Masallaci, Ƴan Sanda Sun Ga Alamu 2 a Wurin

  • Dakarun rundunar ƴan sanda sun gano gawar wata budurwa mai suna Halimat a kusa da wani masallaci a jihar Osun
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sanda ya ce sun samu alamu biyu a wurin, sun ji warin fiya-fiya kuma sun tsinci takarda
  • Ya ce suna kan gudanar da bincike kuma sun samu ganin ɗaya daga cikin ƴan uwanta, wanda ya fara ba su cikakkun bayanai game da mamaciyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Jama'a sun shiga ruɗani da tashin hankali da aka tsinci gawar wata budurwa mai suna Halimat a kusa da Masallaci a jihar Osun yau Litinin.

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Osun ce ta gano gawar Halimat a kusa da wani masallaci da ke unguwar Ogo-Oluwa a Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna yayin wani mummuman hari a Zamfara

An ga gawa a kusa da masallaci a Osun.
Yan sanda sun gano gawar wata Halima a kusa da masallaci a jihar Osun Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Abiodun Ojelabi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun fara tattara hujjoji

Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa an samu wata takarda da ake zargin wasikar kisan kai ce a gefen gawar Halimat.

Ojelabi ya ce bayan samun labarin ganin gawar a bayan masallacin da musulmi ke ibada, rundunar ƴan sanda ta tura jami’an tsaro zuwa wurin nan take domin ɗauko ta.

A cewarsa, dakarun ƴan sanda da suka je ɗauko gawar sun tabbatar da cewa sun ji warin fiya-fiya a wurin.

Yadda aka tsinci gawa a kusa da masallaci

"An gano gawar a bayan wani masallaci da ke yankin Ogo-Oluwa a Osogbo. Jami’anmu da suka je wurin sun ji warin maganin kwari watau fiya-fiya, wanda hakan ya jawo surutu kan abin da ya yi ajalin Halimat.

Kara karanta wannan

Babu dadi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata yayin wani hari a Zamfara

"Haka kuma an samu wani abu kamar takardar wasikar kisan kai a kusa da gawar. Wannan kuma ya kara karfafa zargin cewa watakila ita ce ta kashe kanta,” inji Ojelabi.
Yan sanda sun fara bincike.
Yan sun fara tattara bayanai kan gawar da aka gani a bayan masallaci Hoto: Nigerian Police
Source: Getty Images

Ƴan sanda sun kaddamar da bincike kan lamarin

Ya kara da cewa ba a samu wani alamun rauni ko duka a jikin mamaciyar ba lokacin da aka dauke ta.

“A yayin bincike, ‘yan sanda sun gano wani dan uwanta wanda ya bayar da bayanai da dama game da ita, kuma hakan yana taimakawa wajen binciken da aka fara.”

Ojelabi ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya jawo mutuwar Halimat, rahoton Daily Post.

Matashi ya tono gawar kakarsa a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa ƴan sanda sun kama wani matashi dan shekaru 31 da haihuwa a jihar Neja bisa zargin tono gawar kakarsa ta ɓangaren uwa.

Rahotanni sun bayyana cewa matashin ya tono gawar, sannan kuma ya sare kanta da nufin yin tsafin da boka ya ce masa zai samu maƙudan kuɗi.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ’yan sanda na jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce sun cafke matashin tare da wasu abokan aikinsa a wani otel da ke garin Bida a ranar 19 ga Yuli, 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262