Wahala Ta Tunkaro Ƴan Najeriya, Kamfanin NNPCL Ya Canza Farashin Fetur a Gidajen Mai

Wahala Ta Tunkaro Ƴan Najeriya, Kamfanin NNPCL Ya Canza Farashin Fetur a Gidajen Mai

  • Farashin man fetur ya tashi a gidajen man kamfanin NNPCL da ke jihar Legas da kuma babban birnin tarayya Abuja
  • An ruwaito cewa a yau Litinin, 4 ga watan Agusta, 2025, gidajen man NNPCL a Legas sun kara N50 kan kowace litar fetur
  • A birnin Abuja kuwa an samu ƙarin N65 kan kowace lita ɗaya ta fetur, inda farashin ya tashi daga N890 zuwa N955

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Yayin da ƴan Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa, an sake ƙara farashin kowace litar man fetur a ƙasar nan.

Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL ya ƙara farashin kowace lita ɗaya ta man fetur (PMS) zuwa N915 a jihar Lagos da N955 a babban birnin tarayya Abuja.

Farashin fetur ya tashi a gidajen man NNPCL.
Kamfanin NNPCL ya kara farashin kowace litar man fetur a Abuja da Legas Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar The Cable ta lura da cewa, a ranar Litinin, 4 ga watan Agusta, 2025, gidajen man fetur na kamfanin NNPPL sun canza farashin da suke sayar da lita ga jam'a.

Kara karanta wannan

Talaka bawan Allah: ADC ta fusata da Tinubu zai kashe N712bn a gyaran filin jirgin Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPCL ya ƙara farashin fetur a Legas, Abuja

Gidajen mai mallakin NNPCL sun ƙara farashin kowace lita guda ta fetur daga N865 zuwa N915, wanda ke nuna an samu ƙarin N50 kan kowace lita a jihar Legas.

A rahoton da aka tattara yau Litinin, gidajen man NNPCL da ke Abule Ado, titin Ago Palace Way da ke Okota duk a jihar Legas sun ƙara farashin men feturin.

A babban birnin tarayya Abuja kuwa, gidajen mai na kamfanin NNPCL sun kara farashin litar fetur daga N890 zuwa N955 a kowace lita.

Bayanai sun tabbatar da cewa farashin man ya kai N955 a kowace lita a gidan sayar da fetur na NNPCL da ke titin Kubwa Expressway, Abuja, wanda ke nuna an samu ƙarin N65.

Alƙaluman da hukumar NBS ta fitar

A ranar 31 ga Yuli, Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa mazauna Jahohin Jigawa, Ondo da Lagos ne suka fi biyan farashi mai tsada na man fetur a watan Yuni, 2025.

Kara karanta wannan

Yadda aka samu kusan Naira tiriliyan 1 da za a gyara filin jirgin saman Legas

A daya bangaren kuma, Jihohin Yobe, Kogi da Imo ne suka fi samun mai a farashi mai rahusa, inda aka sayar da lita ɗaya kan N950.60, N986.67 da N987.86 bi da bi, inji hukumar NBS.

Farashin fetur ya ƙara tsada.
An samu ƙarin farashin litar man fetur a Legas da Abuja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A watan da ya gabata, matatar mai ta Dangote ta rage farashin fetur da take sayar wa ƴan kasuwa a rumbunanta zuwa N820 a kowace lita, mako guda bayan ta rage farashin zuwa N840.

Sai dai a yau Litinin, an wayi gari da ƙarin N50 zuwa N65 a gidajen man NNPCL da ke jihar Legas da kuma Abuja, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Shugaban NNPCL na ƙasa ya shiga ofishinsa

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bashir Bayo Ojulari, ya fita aiki a daidai lokacin da ake yaɗa jita-jitar ya yi murabus.

Rahotanni sun nuna cewa Ojulari ya isa ofis dinsa kusan ƙarfe 9:35 na safiyar Litinin, 4 ga watan Agustan 2025, lamarin da ya tabbatar da cewa yana nan a kujerarsa.

A karshen makon da ya gabata ne rahotanni da dama suka bayyana cewa Ojulari ya yi murabus, amma babu wata sanarwa a hukumance har zuwa yau.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262