Sabuwar Ɓaraka Ta Danno cikin ADC ana tsaka da Ƙoƙarin Ganin Bayan APC

Sabuwar Ɓaraka Ta Danno cikin ADC ana tsaka da Ƙoƙarin Ganin Bayan APC

  • Ƙungiyar magoya bayan Peter Obi ta rubuta zungureriyar wasiƙar ƙorafi ga jam'iyyar haɗakar adawa
  • Magoya bayan Obi sun ce ADC ta mayar da ita saniyar ware, kuma ana manyan abubuwa ba tare da ƴaƴanta ba
  • Shugaban kungiyar, Dr. Tanko Yunusa ya ce akwai buƙata Peter Obi ya sa baki kafin lamari ya lalace

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Sababbin matsaloli na ƙoƙarin bayyana a cikin haɗakar jam’iyyu ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar ADC.

An gano haka ne bayan wata wasiƙa da aka ce ta fito daga magoya bayan ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi ga ADC.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi
Akwai alamun sabon rikici a ADC Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Twitter

Punch ta ruwaito a cikin wasiƙar, ƙungiyar ta bayyana damuwa kan abin da ta kira wariya da take fuskanta wajen yanke muhimman shawari a cikin haɗakar.

Kara karanta wannan

PDP ta dura kan Atiku da ya zama jigo a haɗakar adawa ta ADC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana fargabar samun rikici a ADC

An dai ƙaddamar da jam’iyyar ADC a matsayin wata haɗakar siyasa a ranar 2 ga Yuli, 2025, domin fitar da Bola Ahmed Tinubu daga kujerar shugabancin kasa a zaɓen 2027.

Manyan ƴan siyasa kamar su David Mark, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Peter Obi, tsohon gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, na cikin jigon tafiyar.

Jam'iyyar adawa ta ADC
Magoya bayan Obi ma zargin ana nuna masu wariya Hoto: ADC 2027 Coalition
Source: Twitter

Kusan wata guda bayan kaddamarwar, Obi bai shiga jam’iyyar ADC kai tsaye ba duk da an ji sakataren yaɗa labarai na rikon kwarya, Bolaji Abdullahi, ya ce an ɗaga masu kafa.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ta ba Obi da El-Rufai damar su zauna a jam’iyyun da suka fito daga gare su na asali a halin yanzu.

ADC: Magoya bayan Peter Obi sun yi ƙorafi

A wata takarda da aka sanya wa hannu a ranar 29 ga Yuli, 2025, da shugaban ƙungiyar magoya bayan Obi, Dr Tanko Yunusa, ya zaegi haɗakar da nuna masu wariya duk da ƙarfin siyasarsu.

Kara karanta wannan

ADC: El Rufai da manyan ƴan siyasar Kaduna da suka fice daga PDP, APC, suka shiga haɗaka

A cikin wasiƙar an ce:

“Muna rubuto ne a madadin magoya bayan Obi don bayyana ƙorafinmu kan abubuwan da ke gudana a tsarin haɗakar.”
“Ana ware mutanenmu da gangan a kowane mataki.”

Dr. Tanko ya zayyana rashin gayyatar magoya bayan Obi a cikin muhimman shawari da taruka.

Ya ce:

“Mun samu labarin cewa an cire wakilai da ƴaƴanmu daga muhimman taruka da ke yanke manyan hukunci kan makomar haɗakar.”

Shugaban ƙungiyar ya bukaci Peter Obi da ya shiga tsakani cikin gaggawa domin dakile rikicin tun kafin lamarin ya kara tabarbarewa.

2027: Yaron El-Rufa'i ya auna tasirin Obi

A baya, kun samu labarin Bashir El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana ra'ayinsa a kan ɗan siyasar da zai iya buga wa da Bola Tinubu.

Ya ce Peter Obi, na da yiwuwar kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 fiye da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Ya ce idan Peter Obi ya zaɓi mataimaki daga Arewacin Najeriya wanda ke da ƙarfi da kima, hakan zai ƙara masa karfi sosai wajen fuskantar Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng