Kwastam: Za a Sayar wa 'Yan Najeriya Litar Man Fetur a kan N400

Kwastam: Za a Sayar wa 'Yan Najeriya Litar Man Fetur a kan N400

  • Hukumar Kwastam ta kama lita 69,375 na man fetur da gas da aka yi yunkurin fitar da su daga Adamawa da Taraba zuwa ƙasar waje
  • Kwamishinan hukumar yankin Arewa maso Gabas ya ce wannan yunkuri wani ɓangare ne na yaki da fataucin kaya da karya tattalin arziki
  • Kwastam ta gargadi jama’a da su daina kai hari kan jami’anta tare da ƙudurin sayar da man da aka kama ga jama’a a farashi mai rahusa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Adamawa - Hukumar Kwastam ta sanar da cafke fiye da lita 69,000 na man fetur da gas da ake kokarin fitarwa daga Najeriya ta haramtacciyar hanya a jihohin Adamawa da Taraba.

Jami’an kwastam na yankin Arewa maso Gabas ne suka samu wannan nasara a cikin mako shida da suka gabata, karkashin shirin “Operation Whirlwind” na yaki da fataucin kaya.

Kara karanta wannan

Sun aikata manyan laifuffuka: Gwamnati ta kori manyan alkalai 2 daga aiki a Neja

Hukumar Kwastam za ta yi gwanjon man fetur a Adamawa
Hukumar Kwastam za ta yi gwanjon man fetur a Adamawa. Hoto: Nigeria Customs Service
Asali: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa hukumar ta wallafa a Facebook cewa za ta sayar da litar man fetur din a kan N400.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adadin man fetur da kwastam ta kama

Shugaban Kwastam na shiyyar Arewa maso Gabas, Hussain Ejibunu ne ya sanar da fetur din da suka kama a wata ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Yola.

Ya ce jami’an kwastam sun kama jarkoki 2,276 masu girman lita 25 na man fetur da kuma jarkoki 19 na gas na mota da aka ɓoye domin fitarwa ta ɓoyayyun hanyoyi zuwa ƙasar waje.

A cewar shi, hanyoyin da aka fi amfani da su wajen fitar da man sun haɗa da Malabu–Belel, Girei–WuroBokki, Gurin–Fufore, Jam Terry, Maiha, Jimeta da Mubi–Sahuda.

An ƙwace motocin da ke jigilar fetur

Ejibunu ya ƙara da cewa sun kama wasu manyan motoci guda biyu da ake amfani da su wajen jigilar man da aka kama a yankunan da lamarin ke gudana.

Kara karanta wannan

Allah Sarki: Hankula sun tashi da yara 8 suka mutu a hadari bayan nutsewa a kogi

Ya kuma yi gargadi ga wadanda ke kai hari kan jami’an kwastam lokacin da suke bakin aiki, yana mai cewa irin waɗannan hare-hare laifi ne da za a hukunta su da tsauraran matakai.

A cewar shi:

“Ba za mu lamunci kai hari ga jami’anmu ba. Duk wanda ya aikata hakan zai fuskanci hukunci mai tsanaki,”
Yadda hukumar kwastam ta kama man fetur a baya
Yadda hukumar kwastam ta kama man fetur a baya. Hoto: Nigeria Customs Service
Asali: Twitter

Za a sayar da litar fetur a kan N400

Hukumar Kwastam ta ce za a sayar da jarakunan man da aka kama ga jama’a a kan ₦10,000 bisa umarnin gwamnatin tarayya domin rage radadin matsin tattalin arziki.

Hakan na nuni da cewa za a yi gwanjon man fetur din a kan N400 duk lita kasancewar kowace jarka za ta dauki lita 25.

'Yan kasuwa sun rage kudin fetur

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan kasuwar man fetur sun rage farashi kasa da na matatar Dangote da kamfanin NNPLC.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da gasa tsakanin manyan dillaln man fetur da Alhaji Aliko Dangote.

Dillalan mai da suke shigo da fetur daga kasashen wajen sun yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya yi watsi da bukatar Dangote ta hana shigo da kaya daga waje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng