Minista Ya Faɗi Babban Alƙawarin da Tinubu zai Cika kafin Ƙarshen Wa'adinsa
- Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya tabbatar cewa gwamnatin Bola Tinubu na saneda babban alƙawarin da ta yi kafin zaɓe
- Ya ce gwamnatin Tinubu za ta tabbatar ta cika alƙawarin kafin wa'adin shugaban ƙasa ya ƙare a 2027
- Sai dai ya nuna shakku a kan tabbatar da ƴan Najeriya za su samu wuta yadda ya kamata a cikin shekaru huɗu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya ce gwamnatin Bola Tinubu na sane da babban alƙawarin da ta ɗauka a lokacin kamfe.
Adelabu ya bayyana cewa Bola Tinubu zai tabbatar ƴan Najeriya sun samu wadatar wutar lantarki kafin karewar mulkinsa a 2027.

Source: Twitter
Jaridar Punch News ta ruwaito cewa Adelabu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin kaddamar da tashar rarraba wutar lantarki da ke unguwar Ikotun-Egbe a jihar Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu zai cika alkawari kan wutar lantarki
Jaridar The Nation ta wallafa cewa Adelabu ya ce gwamnatin tarayya tana daukar matakai da dama domin magance matsalolin da suka dade suna addabar bangaren wutar lantarki a ƙasar.
Ya ce:
“Gwamnatin Najeriya a yanzu, karkashin mai girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da tsarinta ta fahimci cewa makamashi ne ginshikin ci gaban tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi.
"Ƴan Najeriya za su shaida aikin shugaban kasa wajen tabbatar da cewa kowa na jin daɗin samun wutar lantarki ba tare da katsewa ba kafin ya bar mulki.”
Tinubu ya yi alkawarin samar da wuta
A lokacin yaƙin neman zaɓen 2023, Tinubu ya yi alkawarin cewa zai tabbatar da wutar lantarki ta wadata ba tare da katse wa ba a cikin shekara hudu na mulkinsa.
Sai dai, kwanan nan, Sakataren yaɗa labaran ADC, Bolaji Abdullahi, ya yi tambaya kan ko gwamanti za ta iya cika wannan alkawari

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya cika alkawarin samar da tsaro a Najeriya, an kafa hujja da jihohi 2
Ya ce an ci fiye da rabin wa’adin mulkin Tinubu, amma babu a ga gamsasshen ci gaba ba kan alƙawuran da aka yi wa masu kada kuri’a.

Source: Facebook
Amma a ranar Asabar, Adelabu ya ce duk da cewa watakila ba za a kammala cikakken aiwatar da alkawarin cikin shekara hudu ba, burin Tinubu zai iya tabbata kafin 2027.
Ya ce:
"Domin tabbatar da ci gaba da dorewar wannan ɓangare, gwamnatin tarayya tana ci gaba da daukar matakai daban-daban, kuma hakan ya haifar da gagarumin ci gaba.”
Ya kuma bayyana cewa:
"An jawo hannun jarin fiye da $2bn daga ƙasashen waje domin fadada hanyoyin samar da wutar lantarki."
Jam'iyyar ADC ta dura kan Shugaba Tinubu
A baya, kun ji ADC ta kalubalanci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan gazawarsa wajen cika alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabe na 2023.
Daga cikin abubuwan da Tinubu ya ce zai yi idan an zaɓe shi akwai samar da wutar lantarki ba tare da katsewa ba cikin shekaru hudu na mulkinsa.
A sanarwar da Sakataren Yada Labaran ADC , Bolaji Abdullahi ya fitar, ya ce an ci sama da shekaru biyu a mulkin Tinubu, amma babu wutar da aka yi alkawari.
Asali: Legit.ng
