Cakwakiya: Ƴan PDP Sun Zama Ƴan Takarar APC a Kananan Hukumomi 12 a Rivers
- An samu rudani a Rivers bayan fitar da sakamakon zaben fitar da gwani da aka yi a ƙananan hukumomi da ake shirin gudanar da zaɓe
- Lamarin ya faru ne yayin da wasu ‘yan PDP suka fito a matsayin ‘yan takarar APC a kananan hukumomi 12 daga cikin 23
- Yayin da wasu jam’iyyu da bangaren APC ke tunanin kaurace wa zabe, wasu kuma na kokarin sulhu da hukumar zabe ta RSIEC
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Akwai rudani a Rivers dangane da zabukan kananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga Agusta, 2025, a jihar.
Wasu ‘yan jam’iyyar PDP da ke da katin zama mambobi ne suka bayyana a matsayin ‘yan takarar APC a mafi yawan kananan hukumomin jihar.

Source: Facebook
Zaben kananan hukumomi: An samu rudani a Rivers
Leadership ta lura cewa daga cikin kananan hukumomi 23, ‘yan PDP sun fito a matsayin ‘yan takarar APC a kananan hukumomi 12.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadannan kananan hukumomi sun hada da Asari Toru, Ikwerre, Khana, Tai, Degema, Bonny, Oyigbo, Omuma, Ogu/Bolo, Gokana da Etche.
Majiyoyi suka ce wadanda suka fito a matsayin ‘yan PDP da suka ci zabe a baya sun fito daga Emohua, Port Harcourt da Obio/Akpor.
A lokaci guda, ana ganin cewa manyan jam’iyyu a Rivers na iya kaurace wa zabukan da suka hada da ADC, APP da bangaren APC.

Source: Twitter
Hukuncin kotu kan ƙananan hukumomi a Rivers
A baya, jam’iyyar APP da ke da goyon bayan Gwamna Siminalayi Fubara ta lashe kananan hukumomi 22 cikin 23 a zaben Oktoba 5, 2024.
Sai dai kotun koli ta rusa sakamakon zabukan a ranar 25 ga Fabrairu, 2025 saboda RSIEC ba ta bi tanadin sanarwa na kwanaki 90 ba.
Da yake magana da manema labarai, kakakin ADC a jihar, Chif Luckyman Egila, ya ce har yanzu jam’iyyar ba ta yanke hukunci ba.
Egila ya ce:
“A cikin ‘yan kwanakin nan, za mu yi taron masu ruwa da tsaki don yanke hukuncin shiga ko ficewa daga zaben.”
APC na iya shiga zaɓen ƙananan hukumomi
Haka kuma, kakakin bangaren jam'iyyar APC na Emeka Beke a jihar, Hon. Darlington Nwauju, ya ce shiga zaben ya dogara da warware rikice-rikice.
Nwauju ya ce:
“Mun dauki matsaya bisa wasu kura-kurai da RSIEC ta yi wajen rashin gane sahihin shugabancin APC a jihar.
“Amma bisa tattaunawar da muka yi da shugabancin APC na kasa, muna fatan samun sulhu don ka da a lalata jam’iyya saboda wasu mutane.”
Sharudan Tinubu ga Fubara kan dawowa mulki
Kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya amince da dawo da Gwamna Siminalayi Fubara kan mulki bisa wasu sharuda da ya gindaya.
Daga cikin sharudan akwai cewa ba zai nemi tazarce ba a zaben 2027 mai zuwa a jihar Rivers kuma zai biya yan majalisa.
Har ila yau, Nyesom Wike zai nada shugabannin kananan hukumomi 23, sannan Fubara zai biya hakkokin ‘yan majalisa 27.
Asali: Legit.ng

