Allah Sarki: Hankula Sun Tashi da Yara 8 Suka Mutu a Hadari bayan Nutsewa a Kogi
- Wani hadari ya auku a Jihar Jigawa inda yara mata takwas suka mutu bayan jirgin ruwa ya kife a kogin Zangwan Maje a karamar hukumar Taura
- Yaran 15 ne ke cikin jirgin lokacin da hadarin ya auku da misalin karfe 8:15 na dare, yayin da wata guguwa mai karfi ta tashi wanda shi ne sanadinsu
- Jirgin ruwa ya kife ne sakamakon ambaliya da iska mai ƙarfi, an ceto yara bakwai, sai kuma aka tono gawarwakin yara matan takwas
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dutse, Jigawa - Wani mummunan lamari ya auku a Jigawa inda aka rasa rayuka yara da dama da ya tayar da hankulan al'umma da ke yankin a jihar.
Akalla yara mata takwas suka mutu bayan hatsarin jirgin ruwa dauke da yara 15 ya kife a kogin Zangwan Maje da ke karamar hukumar Taura.

Source: Original
Yawan rayuka da ake radawa a hatsarin jirgi
Zagazola Makama ta tattaro cewa hadarin ya faru ne da misalin karfe 8:15 na dare a ranar Asabar 2 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A Najeriya, ana yawan samun hatsarin jiragen ruwa wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin mutane duk da daukar matakai da ake yawan yi.
A Arewacin Najeriya, an sha samun irin haka a Jigawa, Sokoto da Taraba, Adamawa da kuma jihar Niger wanda aka samu irin haka babu adadi.
Mu annabin faruwar iftila'in hatsarin jirgin ruwan
Lamarin ya faru ne lokacin da yaran ke tafiya daga Zangwan Maje zuwa Jijin Gunka yayin wata iska mai karfi da ruwa mai gudu.
“Yara 15 ne ke cikin jirgin lokacin da ya kife, an ceto yara bakwai da rai, yayin da aka gano gawarwakinsauran takwas, dukkansu mata ne."
- Cewar wasu majiyoyi

Source: Twitter
Hatsarin jirgin ruwa: Ana cikin zullumi a Jigawa
Al'ummar yankin da dama sun kadu da wannan iftila'in da ya afku musamman rasa rayukan yara ƙanana da aka yi sanadin abin da ya faru.
Majiyoyin sun danganta hadarin da cika kogin da kuma iska mai karfi da ta fi karfin jirgin ruwa da ake amfani da shi a yankin.
Wani mazaunin yankin ya ce masu ninkaya a gari da al’umma sun tashi da gaggawa domin ceto rayuka da kuma tono gawarwakin da suka nutse a cikin ruwa.
Hukumomi sun shawarci mutane da su guji ketare koguna masu ruwa da ya yi ambaliya, musamman a damina, tare da amfani da abubuwan kariya.
Sokoto: An rasa rayuka a hatsarin jirgin ruwa
A baya, mun ba ku labarin cewa rahotanni daga hukumar NEMA sun tabbatar da hatsarin kwale-kwale a kauyen Sullubawa da ke ƙaramar hukumar Shagari a jihar Sokoto.
An tabbatar da cewa mutum bakwai ne suka rasa rayukansu a cikin hatsarin da ya auku da safiyar ranar Litinin, 2 ga Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 9:30 na safe.
Rahotannin farko sun nuna iska mai ƙarfi ce ta haddasa kifewar kwale-kwalen a tsakiyar kogin da mutane suke wucewa ta cikinsa wanda ya jawo asarar rayuka.
Asali: Legit.ng

