'Mata da Ke da Budurcinsu Kawai Ya Kamata a ba Sadaki': Reno Omokri Ya Ta da Ƙura
- Tsohon mai taimaka wa shugaban kasa, Reno Omokri, ya ce ya kamata a biya kudin gaisuwa ne kawai ga budurwar da ba ta taba aure ba
- Omokri ya bayyana bambanci tsakanin sadaki da kudin aure, inda ya ce kudin gaisuwa na addini da al'ada ne ga budurwai kawai
- Ya ce al'adun Yarbawa da nassoshin Littafi Mai Tsarki suna nuna cewa budurwa ce kadai ake kira "amarya" kuma ita ake biya mata kudin gaisuwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tsohon mai taimaka wa shugaban kasa, Reno Omokri, ya bayyana wadanda ya kamata a ba sadaki.
Omokri ya ce budurwa ce kawai ya dace a biya musu kudin sadaki lokacin aurensu ba kowa ba.

Source: Facebook
Omokri ya yi bayani kan biyan sadaki
Omokri ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, ta wata doguwar wallafa da ya yi a shafinsa na X, inda ya fayyace batun.

Kara karanta wannan
9ice: An yi wa fitaccen mawaƙin Najeriya sihiri, ya shafe watanni 6 yana aman jini
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, mutane da dama sun rikice da ma'anar sadaki da kudin aure, inda ya ce wadannan kalmomi biyu ba daya ba ne.
Ya ce:
“Akwai bambanci mai girma tsakanin sadaki da kudin da ake ba amarya, kalmomin suna da ma'anoni da tushe daban-daban.
“Sadaki shi ne dukiyar da iyaye ke ba wa 'yarsu mace a ranar aurenta domin ta kai gidan mijinta, ya zama mallakin ma'aurata.
“Wannan al'ada tana gudana a Turai, Asiya da Gabas ta Tsakiya, kuma tana da daidaito da umarnin Littafi Mai Tsarki, Farawa 2:18.”
Ya kwatanta hakan da kudin aure, wanda ya ce yana da tushe a al’adar Afirka da dokar Yahudawa, kuma yana shafi budurwai ne kawai.
“Sadaki daban ne, A al’adar Afirka da Yahudanci, ana biyan iyaye kudin aure ne kawai idan matar budurwa ce."
- Cewar Omokri

Source: Facebook
Omokri ya magantu kan biyan sadaki a al'adu
Omokri ya ce a al’adar Lukumi Yarbawa, idan ba a ga jinin budurci a daren farko ba, sai a mayar da kudin gaisuwa.

Kara karanta wannan
Bayan bidiyon Ummi Nuhu, Mai Dawayya ya yi tone tone, ya faɗi shura da ya yi a baya
Ya caccaki yadda ake yawan bukatar kudi a lokacin aure, musamman idan matar ba budurwa ba ce, yana kiran hakan da “tursasawa.”
Omokri, wanda aka san shi da fahimtar addini, ya ce kalmar “amarya” a Littafi Mai Tsarki na nufin budurwa ne kawai.
Ya kara da cewa:
“Ana bukatar kudi da dukiya da yawa a kan mace da ba budurwa ba, wannan ba kudin gaisuwa ba ne, kwace ne kawai.
“A al’ada da dokar Littafi, namiji na iya auren mace da ba budurwa ba, amma ba za a kira ta amarya ba, ba a biyan kudin gaisuwa.”
Ya bayyana cewa a nan Afrika wasu iyaye na amfani da aure ne don tara kudi daga dangin ango.
An shawarci yan Arewa kan tazarcen Tinubu
Kun ji cewa Reno Omokri ya bukaci shugabannin Arewa su ba Bola Tinubu damar kammala mulkinsa domin zaman lafiyar kasa.
Ya ce a baya an hana shugaba Goodluck Jonathan damar wa'adi na biyu, lamarin da ya haifar da tarzoma a yankin Niger Delta.
Omokri ya ce Arewa na amfana da ayyuka da shirye-shiryen Tinubu, ciki har da manyan tituna da tallafin karatu ga dalibai.
Asali: Legit.ng