Yobe: Bayan Mutuwar Sarki, Gwamna Buni Ya Naɗa Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Sarauta

Yobe: Bayan Mutuwar Sarki, Gwamna Buni Ya Naɗa Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Sarauta

  • Gwamna Mai Mala Buni ya amince da nadin tsohon ɗan majalisa a matsayin sabon Sarkin Gudi, bayan rasuwar marigayi Sarki
  • Sabon Sarkin, Ismaila Ahmed Gadaka ya wakilci Fika/Fune a Majalisar Wakilai daga 2011 zuwa 2019
  • Gwamna Buni ya bayyana kwarin gwiwarsa ga sabon sarki, yana fatan zai kawo ci gaba da zaman lafiya a masarautar Gudi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gudi, Yobe - Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya amince da nadin sabon basarake bayan rasuwar Sarkin Gudi a jihar Yobe.

Gwamna Buni ya nada Hon. Ismaila Ahmed Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi bayan rasuwar Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Kaji.

Gwamna Buni ya naɗa sabon Sarkin Gudi
Gwamna Buni ya naɗa tsohon ɗan majalisa a matsayin sabon Sarkin Gudi. Hoto: Mai Mala Buni.
Source: Facebook

Nadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa Sakataren Gwamnatin Jiha, Shuaibu Abdullahi, ya fitar a ranar Lahadi da safe, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kabiru Gombe ya caccaki Sheikh Jingir bayan malaman Izalar Jos da Kaduna sun hadu

Yobe: Rasuwar Sarkin Gudi ta girgiza al'umma

Wannan nadin na zuwa ne kwanaki uku bayan tabbatar da rasuwar Sarkin Gudi wanda ya yi bankwana da duniya a wani asibiti da ke birnin Abuja.

A ranar Alhamis 31 ga watan Yulin 2025 ne aka sanar da rasuwar Sarkin Gudi, Mai martaba, Alhaji Isa Bunuwo Ibn Madubu Khaji bayan doguwar jinya.

Marigayin wanda aka bayyana a matsayin mai son zaman lafiya ya rasu ne a wani asibiti da ke birnim tarayya Abuja.

Buni ya amince da nadin sabon Sarkin Gudi a Yobe
Bayan rasuwar Sarki, Gwamna Buni ya amince da nadin sabon Sarkin Gudi. Hoto: Mai Mala Buni.
Source: Facebook

Gwamna Buni ya nada sabon Sarki a Yobe

An bayyana cewa sabon sarkin, Mai Martaba Hon. Ismaila Ahmed Gadaka, yana da gagarumar ƙwarewa a bangarorin gwamnati da masu zaman kansu.

Sanarwar ta ce daga shekarar 2011 zuwa 2019, sabon Sarkin ya wakilci mazabar Fika/Fune a Majalisar Wakilai ta Tarayya.

Har ila yau, daga 2007 zuwa 2010, ya rike matsayin kwamishina a cikin gwamnatin jihar Yobe kafin ya koma Majalisar Wakilai.

Kara karanta wannan

Kano: Minista ya faɗi wanda suke son ba takara a APC domin ƙwace kujerar Abba

Sanarwar ta ce:

"Sabon Mai Gudi ya kasance gogaggen jami’in banki, inda ya yi aiki a UBA da Standard Trust har ya kuma zama Manajan Kasuwanci.
“Ya kuma nuna bajintar shugabanci a matsayin Shugaban Kwamitin Kula da Ayyukan ƙananan hukumomi na Yobe da Shugaban Hukumar Kwalejin Ilimi ta Yawuri."

Mukamin sabon Sarkin kafin nadin sarauta

Majiyoyi sun tabbatar da cewa kafin nada shi wannan babbar sarauta. Hon. Gadaka shi ne Yariman Gudi, Daily Post ta ruwaito.

“Har zuwa nadin da aka yi masa a matsayin Sarkin Gudi, yana riƙe da sarautar Yariman Gudi wanda ke nuna zurfin alakar sa da masarautar.
“Gwamna Buni ya bayyana kwarin gwiwa cewa sabon Sarkin zai kare kimar masarautar Gudi tare da kawo zaman lafiya da ci gaba a jihar.”

- Cewar sanarwar

An nada sabon Sarkin Gusau a Zamfara

Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin jihar Zamfara ta nada Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: An shiga jimami bayan Sarkin Gudi ya yi bankwana da duniya

Sarkin Katsinan Gusau, Mai Martaba Ibrahim Bello, ya koma ga Mahalicci a safiyar ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, 2025 yana da shekara 71.

Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da cewa an yi nadin ne bisa doka da kuma shawarar masu zaben Sarki a masarautar Gusau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.