'Yan Sanda Sun Yi Musayar Wuta da 'Yan Bindiga a Katsina, An Dakile Hare Hare 2

'Yan Sanda Sun Yi Musayar Wuta da 'Yan Bindiga a Katsina, An Dakile Hare Hare 2

  • Rundunar ‘yan sandan Katsina tare da hadin guiwar sojoji da askarawa sun dakile hare-hare biyu a kauyuka uku na Faskari
  • Bayan samun bayanan sirri daga Faskari, jami’an tsaro sun yi gaggawar kai dauki tare da fatattakar ‘yan bindiga bayan musayar wuta
  • Kwamishinan ‘yan sanda CP Bello Shehu ya jinjinawa jami’ansa tare da bukatar hadin kan al’umma don samar da cikakken tsaro a jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta dakile harin wasu ‘yan bindiga a kauyuka uku da ke cikin karamar hukumar Faskari.

A cewar sanarwar da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar, an kai hare haren biyu ne a kauyukan Unguwar Dudu, Yartasha da Buntu.

'Yan sanda, sojoji, 'yan sa kai da askarawa sun dakile hare-hare biyu na 'yan bindiga a Katsina
Jami'an rundunar 'yan sanda sun fita sa ido da tsaurara tsaro a lokacin bikin babbar sallah a Katsina. Hoto: @KatsinaPoliceNG
Source: Twitter

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 2 ga watan Agusta, 2025, kamar yadda aka bayyana a cikin sanarwar da aka wallafa a shafin rundunar na X.

Kara karanta wannan

2027: Dino Melaye da wasu na hannun daman Atiku 2 da suka fice daga PDP zuwa ADC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Katsina: 'Yan sanda sun fafata da 'yan ta'adda

Legit Hausa ta tattaro cewa da misalin karfe 3:00 na rana, ofishin ‘yan sanda na Faskari ya samu bayanan sirri cewa wasu ‘yan bindiga dauke da miyagun makamai na shirin kai hari a Unguwar Dudu.

"Nan take, DPO na Faskari ya hada rundunar hadin gwiwa da ta kunshi jami’an ‘yan sanda, sojoji, askarawan Katsina (KSCWC), da yan sa-kai, inda suka isa yankin tare da dakile harin."

- DSP Abubakar Sadiq Aliyu.

A wani lamarin kuma, rundunar ta ce da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Asabar din, ta samu wani rahoto cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyukan Yartasha da Buntu a cikin karamar hukumar Faskari.

Jami’an tsaro da suka hada da rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) sun yi gaggawar tunkarar lamarin. An shiga artabu da ‘yan bindigar, inda aka yi nasarar fatattakar su daga yankin.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP, an tura miyagu barzahu

Kwamishina ya jinjinawa 'yan sanda

Da yake tsokaci kan lamarin, kwamishinan ‘yan sandan Katsina, CP Bello Shehu, ya yaba da daukin gaggawar da jami’an suka kai don dakile harin.

Ya kuma sake jaddada kudirin rundunar ‘yan sanda na ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro da al’umma domin tabbatar da tsaro a fadin jihar.

CP Shehu ya bukaci jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanai cikin lokaci domin dakile laifuka da inganta zaman lafiya a cikin al’umma.

Kwamishinan 'yan sanda, CP Bello Shehu ya sha alwashin hada kai da jami'an tsaro don kare rayuka da dukiyoyi a Katsina
Kwamishinan 'yan sandan Katsina, shugaban hukumar NSCDC da wasu jami'an tsaro a lokacin jana'izar Buhari. Hoto: @KatsinaPoliceNG
Source: Twitter

An jinjinawa jami'an tsaro a Katsina

Wani masanin tsaro daga jihar Katsina mai amfani da suna @Bakatsine a shafin X, ya yabawa ‘yan sanda bisa nasarar dakile harin ‘yan bindiga biyu a rana guda a Faskari.

Ya ce:

“Godiya ga ‘yan sanda na Katsina bisa kwarewar dakile harin ‘yan bindiga biyu a rana daya a Faskari. Irin wannan jarumtar ce muke bukata a yankunanmu.
"Allah ya kare jami’an tsaro da ke bakin kokarinsu wajen dawo da zaman lafiya na dindindin.”

Kara karanta wannan

An gwabza fada tsakanin 'yan sanda da 'yan ta'adda a Katsina, an rasa rayuka

An fafata tsakanin 'yan sanda da 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar ‘yan sanda a Katsina ta dakile yunkurin sace mutane a Katsina har sau biyu, inda aka ceto mutane 28.

A harin farko da aka kai daren ranar Lahadin makon jiya, ‘yan sanda sun kubutar da wasu mutane 14 da aka sace a Sabuwa tare da kwato shanu biyu.

A hari na biyu a safiyar Talatar makon jiya, ‘yan sanda sun sake fatattakar ‘yan bindiga bayan samun kiran gaggawa daga wani mai kishin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com