Ojulari: EFCC da DSS Sun Kwamushe Shugaban NNPCL? An Ji Yadda Lamarin Yake

Ojulari: EFCC da DSS Sun Kwamushe Shugaban NNPCL? An Ji Yadda Lamarin Yake

  • Ana ta yada jita-jita cewa hukumomin EFCC da DSS sun dauke shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari
  • Majiyoyi daga hukumomin biyu sun fito sun musanta cewa sun tilastawa shugaban na NNPCL yin murabus daga mukaminsa
  • Wata majiya daga EFCC ta bayyana cewa waau masu zanga-zanga sun shigar da korafi a wajen hukumar kan Bayo Ojulari

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta ƙaryata zarge-zargen da ke cewa ta yi garkuwa da shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari,

Hukumar EFCC ta kuma musanta cewa ta tilasta masa yin murabus, biyo bayan jita-jitar da ke yawo kan saukarsa daga mukamin shugabancin NNPCL.

EFCC ta musanta dauke shugaban NNPCL
EFCC ta ce ba dauke shugaban NNPCL ba Hoto: @nnpclimited
Asali: Twitter

Wani babban jami’i daga cikin EFCC ya tabbatar wa jaridar The Punch cewa hukumar ta karɓi ƙorafi a kan shugaban na NNPCL.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPCL ya yi murabus saboda zargin satar N34bn? Majiya ta fayyace gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Asabar, jita-jitar cewa an tsare Ojulari kuma an tilasta masa yin murabus ta bazu a kafafen sada zumunta.

Wasu rahotanni sun ce shugaban EFCC, Ola Olukoyede, da darakta janar na hukumar tsaro ta DSS, Adeola Ajayi, sun matsa masa lamba har ya sa hannu a takardar murabus.

Me EFCC da DSS suka ce kan dauke Ojulari?

Wani babban jami’in EFCC da ya nemi a sakaya sunansa, ya ƙaryata rahoton cewa an tilastawa Bayp Ojulari yin murabus.

"Labaran ƙarya ne waɗanda ba su da tushe. Ba gaskiya ba ne cewa EFCC ta yi garkuwa da Ojulari. A ranar Alhamis wasu masu zanga-zanga sun zo ofishinmu da ƙorafi, suna so hukumar ta binciki shugaban NNPCL."
"Wadannan mutane suna da ’yancin miƙa ƙorafi. Mun shaida musu cewa za mu duba ƙorafin. To, ina aka ce an yi garkuwa? Ya kamata mutane su daina bazar jita-jita mara tushe."

- Wani jami'in EFCC

Kara karanta wannan

'Ta zama fanko,' NNPP ta dura kan PDP da ta soki mulkin Abba a Kano

Haka kuma, wani babban jami’in DSS ya musanta zargin cewa darakta janar na hukumar ya shirya wani irin ‘juyin mulki’ don sauke Bayo Ojulari daga mukaminsa ba bisa ƙa’ida ba, rahoton TheCable ya tabbatar

Jami’in, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya bayyana zargin da cewa babu gaskiya a cikinsa.

"DSS ba ta da wani hannu cikin wannan zargi. A gaskiya ma, shugabanmu da aka ambata a cikin zargin bai da hannu kwata-kwata."

- Wani jami’in DSS

Manya na jin haushi Bayo Ojulari
Bayo Ojulari bai sauka daga mukaminsa ba Hoto: @nnpclimited
Asali: Facebook

Wasu manya na jin haushin Bayo Ojulari

Sai dai wasu majiyoyi daga cikin NNPCL sun bayyana cewa akwai alamun cewa wasu mutane a cikin fadar shugaban ƙasa ba sa jin daɗin salon shugabancin Bayo Ojulari.

Ba kamar magabacinsa ba, an ce Ojulari yana tafiyar da NNPCL ne a matsayin kamfani na kasuwanci kawai, yana ƙin yadda ana matsa lamba da buƙatun siyasa.

A kwanan nan, korar manyan jami’an kamfanin da ya yi, ta haifar da fargaba tsakanin wasu fitattun jami’an gwamnati da ’yan siyasa masu alaƙa da waɗanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Masana'antar fina finan Najeriya ta yi rashi, matashiyar jaruma ta riga mu gidan gaskiya

Majiyoyin sun ƙara da cewa Bayo Ojulari yana fuskantar zargi da yin hulɗa da wani ɗan siyasa mai tasiri daga cikin ’yan adawa a ƙasar.

Sai dai, ƙoƙarin samun sahihan bayanai daga NNPCL kan jita-jitar murabus ɗinsa bai yi nasara ba, domin kamfanin bai naɗa sabon mai magana da yawunsa ba bayan saukar Olufemi Soneye daga mukamin.

Kamfanin NNPCL ya tono rijiyoyin mai a Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), ya tono rijiyoyin mai a jihar Bauchi da ke yankin Arewa.

Wani darakta a kamfanin NNPCL, Yusuf Usman, ya bayyana cewa an kammala hako rijiyoyon mai guda hudu a yankin Kolmani.

Ya jaddada cewa kamfanin zai ci gaba da aikin hako mai da iskar gas a yankin Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng