Asiri Ya Tonu: 'Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Hana a Kashe Bello Turji a Zamfara'
- Sani Shinkafi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dakile rundunar CJTF da CPG daga kashe Bello Turji a Zamfara
- Mai sharhi kan lamurran tsaron ya ce CJTF da CPG na dab da shafe babin Turji, gwamnatin tarayya ta ce su koma Shinkafi
- A cewarsa, gwamnatin tarayyar ta ce za ta yi sulhu da shugaban ƴan ta'addar, abin da Bello Turji ya ƙi amincewa da shi
- Fadar shugaban ƙasa ko ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro (NSA) ba su yi martani kan kalaman Shinkafi ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Sani Shinkafi, kwararre kan sha’anin tsaro, ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ce ta hana a kashe ko a kama shugaban ’yan ta’adda, Bello Turji.
Masanin tsaron, ya yi ikirarin cewa, rundunar hadin gwiwa ta fararen hula (CJTF) sun samu damar kashe Bello Turji a jihar Zamfara amma aka dakatar da su.

Kara karanta wannan
Amnesty Int'l ta dura kan Tinubu da gwamnati ta ƙi tsoma baki shekaru 6 da 'sace' Dadiyata

Source: Facebook
Sani Shinkafi, wanda tsohon shugaban kwamitin tsaro da gurfanar da ’yan bindiga ne a Zamfara, ya fadi hakan ne a yayin hira da Channels TV a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matsalar 'yan bindiga a jihar Zamfara
Kamar yadda ake fama da hare-haren ’yan ta’adda a Sokoto, jihar Zamfara ma na cikin jihohin da ke fama da hare-hare daga wasu miyagun ’yan bindiga.
An kashe daruruwan mutane, an karɓe miliyoyin Naira na kuɗin fansa tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu a sakamakon hare-haren.
An ce Bello Turji ne ke jagorantar da dama daga cikin wadannan ’yan bindiga, inda suke kakaba haraji da kuma hallaka mutane a jihohin Zamfara da Sokoto.
A kokarin dakile wannan matsala, gwamnatin Zamfara ta dauki dubban matasa aiki a rundunar CJTF domin taimakawa jami’an tsaro na gwamnati wajen yaki da ta’addanci.
A watan Janairun 2024, gwamnatin jihar ta kafa rundunar Askarawa ta CPG domin inganta yaki da ta’addanci a yankin.
“Yadda aka hana kashe Bello Turji” – Shinkafi
Sani Shinkafi ya bayyana cewa an kusa hallaka Bello Turji lokacin da wasu shugabannin kauyuka suka tura dakarun CJTF da CPG zuwa dajin da ke karamar hukumar Shinkafi domin fafatawa da ’yan bindigar.
“A lokacin da suka fara fada, sun kusa gamawa da shi (Bello) Turji. An kashe da dama daga cikin mayakansa a wannan artabun.
“Amma gwamnatin tarayya ta dakatar da farmakin. Ta ba su umarnin su koma Shinkafi, da cewar za ta bi hanyar sulhu da Bello Turji.
“A daidai lokacin da rundunar fararen hula ke samun nasara, da gwamnatin ta basu dama su ci gaba da yakin, da yanzu da an shafe Turji daga doron ƙasa."
- Sani Shinkafi.
Shinkafi ya kara da cewa daga bisani Bello Turji ya ki amincewa da sulhun da wasu shugabannin al’umma da na addini suka jagoranta, saboda babu Gwamna Dauda Lawal a cikin tattaunawar.

Source: Facebook
Gwamnatin tarayya ba ta ce komai ba

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya cika alkawarin samar da tsaro a Najeriya, an kafa hujja da jihohi 2
Kodayake bai bayyana ainihin ranar da lamarin ya faru ba, alamu na nuna cewa hakan ya faru ne tsakanin karshen 2024 zuwa farkon 2025.
A yayin da aka tuntube shi a ranar Alhamis, mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya tura wakilin Premium Times zuwa ga Usman Zakari, hadimin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu.
Sai dai Usman Zakari bai yi martani kan kalaman Sani Shinkafi ba, saboda bai ba da amsar sakkonin tes ko kuma amsa kiraye-kirayen waya da aka yi masa ba.
Gwamnati ta kafawa Bello Turji sharuɗɗa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Sokoto ta yi magana kan sulhu da ake shirin yi da yan bindiga bayan hare-haren da ake kai wa.
Gwamnatin ta bukaci hatsabibin jagoran ƴan bindiga, Bello Turji da ya saki dukkan fursunonin da ke hannunsa.
Mai bai wa Gwamna Ahmed Aliyu shawara, Kanal Ahmed Usman mai ritaya, ya ce furucin Turji na neman zaman lafiya ba zai yi tasiri ba.
Asali: Legit.ng
