Ta Fara Tsami tsakanin Ministan Tinubu da Gwamna, An ci Gyaran Bago kan Matakinsa
- Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya ci gyaran Gwamna Mohammed Umaru Bago kan matakin da ya ɗauka
- Idris ya ce gwamnonin jihohi ba su da hurumin rufe gidajen rediyo, sai hukumar NBC ce kaɗai ke da wannan iko
- Bago ya rufe Badeggi FM bisa zargin ta da hankali, amma hakan ya haifar da ce-ce-ku-ce daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya ja kunnen gwamna kan shiga hurumin da ba nashi ba.
Idris ya bayyana cewa Hukumar Kula da yada labarai ta ƙasa (NBC) ce kaɗai ke da hurumin dakatar da lasisin gidajen rediyo.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Rabiu Ibrahim wanda ma'aikatar ta wallafa a Facebook a ranar Asabar 2 ga Agusta, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin da Bago ya dauka kan gidan rediyo
Ministan tarayyar a yi tsokaci kan batun bayan Bago, ya bayar da umarnin rufe tashar Badeggi FM da ke Minna.
Gwamnan ya ɗauki matakin bayan zargin yada shirye-shiryen da suka saba da ƙa’ida da ta da zaune tsaye.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin karɓe lasisin tashar, da binciken wanda ke da ita, tare da umartar Kwamishinan Tsaro da Kwamishinan ’Yan Sanda da su kulle tashar.
Wannan matakin gwamnatin jihar ya jawo ce-ce-ku-ce daga kungiyoyi daban-daban, inda masu kare haƙƙin ɗan Adam da masu rajin ’yancin jarida suka bayyana damuwarsu.

Source: Facebook
Niger: Kungiyar Amnesty ta yi Allah wadai
Kungiyar Amnesty International ta ce umarnin da gwamnan ya bayar 'ba bisa doka ba ne' tana mai cewa gwamna Bago ba shi da ikon rufe tashar rediyo.
A cikin wata sanarwa da Isa Sanusi, Daraktan Amnesty International na Najeriya ya fitar, kungiyar ta ce umarnin rufe gidan rediyon ba shi da tushe kuma ba za a iya kare shi ba, cewar Punch.
Sanusi ya soki yadda gwamnatin jihar ke mai da hankali wajen danniya ga kafafen yada labarai, duk da tabarbarewar tsaro, ciki har da kashe-kashe.
Minista ya ci gyaran gwamna Umar Bago
Yayin da yake maraba da matakin Gwamnatin Niger na kai ƙarar Badeggi FM bisa zargin aikata laifi, ma’aikatar ta jaddada cewa NBC ce kaɗai ke da ikon dakatarwa.
Ministan ya roƙi dukkan ɓangarorin da su kwantar da hankali, yana mai tabbatar da cewa:
“NBC na da hanyoyin warware irin wannan matsala bisa adalci da gaskiya.”
Gwamna Bago ya maka gwamnatin Tinubu a kotu
Mun ba ku labarin cewa gwamnatin jihar Niger karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Umar Bago ta shigar da gwamnatin tarayya kara a gaban kotun koli.
Gwamnatin jihar ta shigar da karar ne kan kin sanya ta cikin jerin jihohin da ke samun kaso 13% na daga abin da aka samu daga albarkatun da suke samarwa.
Gwamnatin ta bukaci kotun da ta umarci a sanya ta cikin jerin, duba da irin dumbin albarkatun da take samarwa ga tattalin arzikin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

