Batun Abba Kyari Ya Girma, an Roƙi Tinubu Alfarma game da Tsohon Ɗan Sandan

Batun Abba Kyari Ya Girma, an Roƙi Tinubu Alfarma game da Tsohon Ɗan Sandan

  • Hukumar kare hakkin dan Adam ta IHRC ta tura alfarma wurin Shugaba Bola Tinubu game da zargin Abba Kyari
  • IHRC ta bukaci afuwa ga Abba Kyari, tana cewa hakan zai taimaka wajen tsaro da kwanciyar hankali
  • Hukumar ta jaddada cewa ba don hana shari’a take nema ba, amma don amfanin kasa idan an tabbatar da cancanta bisa doka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - An tura bukata ta musamman ga shugaban kasa, Bola Tinubu game da zargin da ake yi wa DCP Abba Kyari.

Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Duniya (IHRC) reshen Najeriya ta bukaci a yi wata tattaunawa ta kasa don yi masa afuwa.

An roki Tinubu alfarma game da zargin Abba Kyari
An roƙi Tinubu ya yi wa Abba Kyari afuwa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Abba Kyari.
Source: UGC

Abba Kyari: Hukumar IHRC ta roki Tinubu

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Jakada (Dr.) Duru Hezekiah, shugaban hukumar a Najeriya ya fitar a Abuja, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Za a caɓa: Gwamnatin Tinubu ta fara ɗiban matasa aiki domin rage zaman banza

IHRC ta ce tana girmama shari’ar da ake yi wa DCP Abba Kyari amma wannan kiran ba don shafar hukunci ba ne, sai dai don amfanin kasa gaba daya.

Sanarwar ta ce:

“Matsayinmu ba na karya shari’a ba ne ko tsoma baki cikin tsarin kotu. Sai dai muna so a duba mafita ta gaba bisa doka da tsarin mulki.”

Hukumar ta kara da cewa za a iya duba yiwuwar afuwa ta musamman kamar yadda sashe na 175 na kundin tsarin mulki na 1999 ya tanada.

“A duniya akwai misalai da dama inda wadanda aka yanke wa hukunci aka sake daukar su aiki don kwarewarsu ta taimaka wajen tsaron kasa.
“A Amurka, hukumomin tsaro su kan ba da rangwame ko jinkirin hukunci don su amfana da bayanai daga wadanda suka san harkar sosai.
“A wasu kasashen Afirka da suka fito daga yakin basasa, an taba bai wa tsofaffin shugabannin yaki afuwa ta sharadi don zaman lafiya.”

Kara karanta wannan

'Wanda ya kamata ya zama ɗan takarar ADC tsakanin Atiku, Obi da Amaechi'

- Cewar sanarwar

An bukaci Tinubu ya yi afuwa ga Abba Kyari
Hukumar IRHC ta roki Tinubu afuwa ga Abba Kyari. Hoto Abba Kyari.
Source: UGC

Musabbabin neman afuwa ga Abba Kyari

IHRC ta bayyana cewa irin wannan afuwa ba tana nufin a yafe musu ba ne, amma tana da amfani matuka ga tsarin tsaron kasa da zaman lafiya, The Guardian ta ruwaito.

Ta kara da cewa:

“Afuwa ta sharadi ga Kyari, bisa kulawar jama’a, na iya zama wata dama ta amfani da kwarewarsa a yaki da laifi."

Hukumar ta ce Shugaba Bola Tinubu yana da dama ta tarihi domin jagorantar wannan mataki da goyon bayan al’ummar Najeriya.

Hukumar ta yi kira ga kungiyoyi, lauyoyi, masu kare hakki da masu tsara manufofin tsaro da su fara tattaunawa mai amfani a kai.

Ta ce:

“Muna rokon a sake duba wannan batu ba don son kai ba, amma domin bunkasa tsarin tsaro ta hanyar da doka ta tanada.

Iyalan Abba Kyari sun magantu kan kadararsa

Mun ba ku labarin cewa iyalan Abba Kyari sun karyata zargin yana da asusun banki guda 10 da N200m, inda suka ce labarin karya ne.

Kara karanta wannan

An cakawa jami'ar NSCDC wuƙa a Abuja, asibitoci sun ƙi karɓarta har ta mutu

Sun bayyana cewa yana da asusu a bankuna hudu ne kawai da jimillar kudin da bai kai N4m ba kacal.

Shaida a kotu ya tabbatar babu wata alaka tsakanin kudin asusun Kyari da wata haramtacciyar hulɗa ko laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.