Gaba da Gabanta: Kotu Ta Nuna Iko bayan Hana Gwamna Zaɓe da Naɗa Sarki a Jiharsa
- Wata kotu a garin Okitipupa ta yi hukunci kan karar da aka shigar da gwamna inda ya gargade shi kan nada Sarki
- Kotun ta hana Gwamna Lucky Aiyedatiwa nada sarki a Alagbon a karamar hukumar Ilaje a jihar Ondo
- Kotun ta dakatar da gwamnati da masu ruwa da tsaki daga daukar mataki bayan an amince da Ajaka a matsayin Gbogunron na Idi-Ogba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Akure, Ondo - Kotun da ke sashin Okitipupa a jihar Ondo ta dakile ikon gwamna kan nadin Sarki.
Kotun ta dakatar da Gwamna Lucky Aiyedatiwa daga zabe, amincewa ko nada wani Sarki a garin Alagbon.

Source: Twitter
Kotu ta dakile ikon gwamna a nadin Sarki
Rahoton Tribune ya ce Alagbon na cikin masarautar Ugbo da ke karamar hukumar Ilaje a jihar Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari’a Adedipe ne ya bayar da umarnin dakatarwa a ranar Juma’a 1 ga watan Agustan 2025.
Kotun ta hana dukkan wadanda ake kara daukar wani mataki da zai iya shafar yadda za a yanke hukuncin karar da ke gaban kotun.
Hakan na zuwa ne bayan Gwamna Aiyedatiwa ya tabbatar da nadin Prince Olusola Joseph Ajaka a matsayin Gbogunron na farko na Idi-Ogba Alagbon.
Bayan zaman majalisar zartarwa ta jihar, kwamishinan kananan hukumomi da al’amuran sarauta, Alhaji Amidu Takuro, ya bayyana nadin a hukumance.
Takuro ya ce:
"An bi ka’ida wajen nadin Ajaka kuma ya biyo bayan shawarwarin da hukumomin gargajiya suka bayar."

Source: Original
Umarnin da kotu ta bayar a Ondo
Sai dai daga bisani, shugabannin Alagbon suka garzaya kotu domin dakatar da wannan mataki da kuma rushe abin da aka riga aka yi.
Mai gabatar da kara D.J. Ayenowo daga ofishin lauyoyi na Sola Ebiseni ya shigar da bukatar dakatarwa a shari’a mai lamba HOK/76/2022.
Kotun ta ba da umarnin dakatar da gwamnati, wakilanta da kuma duk wanda ke da ruwa da tsaki daga ci gaba da wannan shirin nadin sarki, cewar The Nation.
Wadanda ake kara sun hada da gwamna, Atoni-janar, kwamishinan al’amuran sarauta, sakataren Ilaje, da kuma Olugbo na Ugbo, Oba Akinruntan.
Masu karar sun hada da Chif Isaiah Adewole Demehin, tsohon kwamishina da Asogbon na Ugbo, da Chif Mallon Ogede, Baale na Alagbon.
Sun kalubalanci yunkurin gwamnatin jihar na nada sarki daga dangin Gbogunron wanda suka ce ba da yardar al’ummar Alagbon aka yi ba.
Al’ummar sun kara da zargin wani kwamishina daga dangin Gbogunron da amfani da matsayinsa wajen tilasta gwamnati ta nada 'yan gidansu a matsayin sarki.
Kotu ta kori karar neman tsige Gwamna Aiyedatiwa
Kun ji cewa kotun koli da ke Akure, babban birnin jihar Ondo ta kawo ƙarshen shari'ar da aka ƙalubalanci nasarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa.
A zaman yanke hukunci ranar Alhamis, kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Aiyedatiwa na APC a zaɓen da ya gudana a watan Nuwamba, 2024.
Wannan nasara da gwamnan ya samu ta biyo bayan hukuncin da kotun daukaka kara da kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamna suka yanke a baya.
Asali: Legit.ng

