Musulmi Sun Fusata da Dodon Gargajiya Ya Farmaki Limamin Musulunci, an Roki Gwamna
- Wani dodon gargajiya ya kai hari ga wani Liman a Ogbomoso, inda ya cire masa hula yayin da yake kan babur
- Kungiyar Muslim Public Affairs Centre (MPAC) ta ce hakan saba wa doka ne kuma gwamnati ta binciki Lobanika da dukan masu hannu
- MPAC ta bukaci a daina amfani da bukukuwan gargajiya wajen tauye hakkin jama’a da takura musu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ogbomoso, Oyo - Kungiyar Muslim Public Affairs Centre (MPAC) ta nuna takaici kan kai hari da aka kai kan liman.
Kungiyar ta bayyana takaicinta kan harin da wani dodon gargajiya mai suna Lobanika ya kai wa wani Liman a Ogbomoso a jihar Oyo.

Source: Facebook
Cin zarafin da aka yiwa limamin Musulunci
Daily Trust ta ce lamarin ya faru a kwanakin baya a Oja'gbo, Ogbomoso, inda dodon ya cire hular Liman yayin da yake kan babur ba tare da wani dalili ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bayyana dodon da cewa yana da ɗabi’ar tashin hankali, inda har ya dawo baya domin ganin yadda Liman ɗin zai mayar da martani.
Shugaban Limaman Ogbomoso, Sheikh Teliat Ayilara da wasu malaman addini sun bayyana abin da ya faru a matsayin cin zarafi da rashin mutunci.
MPAC ta bayyana cewa irin wannan cin zarafi ya nuna yadda wasu ke raina hakkin bil’adama da dokar kasa cikin girman kai.

Source: Original
Hari kan liman: Abin da kungiar MPAC ta ce
Shugaban MPAC, Disu Kamor, ya ce wannan lamari yana nuna yadda wasu ke amfani da bukukuwan al’ada wajen gallaza wa mutane ba tare da hukunci ba.
Kamor ya ce sanarwar kungiyar Oloolu a Ibadan da ta haramta wa mata shiga wasu wurare da tilasta wa maza sanya sutura irin tasu, saba wa doka ne.
Ya ce babu wata kungiya, gargajiya ko addini da ke da hurumin tauye hakkin dan kasa a Najeriya kamar yancin tafiya ko sutura.
MPAC ta bukaci ‘yan sanda su binciki lamarin tare da gurfanar da Lobanika da duk wanda ke da hannu a harin da aka kai, cewar Daily Post.
Kungiyar MPAC ta roki gwamna Makinde
Kungiyar ta roki gwamnatin jihar Oyo da ta sanya doka kan bukukuwan dodannin domin kare ‘yancin jama’a da tabbatar da zaman lafiya a gari.
Ta kuma yi kira ga Musulmai da su zauna lafiya, amma ka da su dauki hakuri a matsayin rauni ko yarda da zalunci.
A cewar MPAC, Najeriya mallakin kowa ce, kuma babu wata kungiya da ta fi karfin doka.
Kungiyar ta ce za ta ci gaba da sa ido kan irin waɗannan lamura tare da goyon bayan kare martaba da hakkin Musulmai da sauran jama’a.
Ana zargin Sarki da kokarin hana Musulunci
A baya, kun ji cewa wasu masu shigar dodanni sun kai hari kan gidan limamin gari a Ondo da kuma masallacinsa, inda suka lakada wa iyalansa duka.
Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta soki harin, ta kira shi da barna, rashin hankali kuma abin ta da hankali tare da neman a hukunta masu laifin.
Farfesa Ishaq Akintola ya ce maimakon Sarkin ya hukunta masu laifi, sai ya ci tarar limamin da iyalinsa, tare da barazanar kora.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

