Ikon Allah: Bidiyon wani ‘dodo’ da ya jagoranci al’umman Musulmi a sallah

Ikon Allah: Bidiyon wani ‘dodo’ da ya jagoranci al’umman Musulmi a sallah

  • Wani bidiyo da aka wallafa a shafin soshiyal midiya ya sa mutane yin cece kuce
  • A cikin bidiyon wanda aka wallafa a Facebook, an gano wani dodo yana jagorantar mabiyansa a yayin da suke Sallah
  • Mutane da dama sun yi sharhi inda abun bai yi wa wasu dadi ba ganin dodo yana jagorantar Musulmai Sallah

An dauki wani mutum yayin da yake jagorantar Musulmai Sallah cikin shiga ta dodanni.

A bidiyon da Oloye Omo-Iya Kunmi ya wallafa a Facebook, an gano dodon tare da mabiyansa a saman dadduma suna bautawa Allah.

Ikon Allah: Bidiyon wani ‘dodo’ da ya jagoranci al’umman Musulmi a sallah
Ikon Allah: Bidiyon wani ‘dodo’ da ya jagoranci al’umman Musulmi a sallah Hoto: Oloye Omo-Iya Kunmi
Asali: Facebook

Da yake wallafa bidiyon, Kunmi ya rubuta cewa:

“Barka da Juma’a ya al’umman Musulmi. Ramoni ya kasance cikin wannan shiga!”

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke dan bindigan da ya sace daliban Kwalejin Noma na Afaka

Yayin da ake gudanar da sallar, an jiyo mutumin da ke daukar bidiyon yana jinjinawa wani amma hakan bai ja hankalin dodon da sauran Musulmai da ke sallah ba.

Mabiya shafin soshiyal midiya sun yi martani

‘Yan Najeriya a Facebook sun je sashin sharhi na wallafar don bayyana ra’ayinsu yayin da dama suka dara bayan kallon bidiyon.

Da yake martani wani mai suna Samsudeen Mobolaji Popoola ya ce:

“Menene mutum ba zai gani ba a kauyen Oyo?"

Abiola Enuoranoba Obinrin ya rubuta:

"Ku cigaba dai."

prince Raji Hammed Frank yayi sharhi:

"Ka ji irin wannan matakin, bai dace ba walahi."

Abeshin Adebimpe Adukeade ya ce:

"Matsala ba ya karewa.”

Kotu ta bada umurnin a tsare 'dodo' saboda zargin kisa bayan kai hari masallaci

A wani labari, wata kotun majistare da ke Osogbo, jihar Osun ta bada umurnin a tsare mata Fashola Esuleke, dodon da ke da hannu cikin fadar da ta yi sanadin rasuwar Alhaji Moshood Salahudeen a masallacin Kamorudeen a babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisar PDP sun zargi Jami’an tsaro da hada-kai da ‘Yan bindiga a jihar Arewa

Daily Trust ta ruwaito cewa an tsare Esuleke ne tare da Kazeem Yunus, babban limamin masallacin da huɗu daga cikin mabiyansa.

An gurfanar da limanin ne saboda dukan dodon yayin da an gurfanar da dodon bisa zargin kisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel