'Na So Ya Fi Haka': Tsohon Gwamna Ya Koka kan Tattalin Arziki yayin ba da Gudunmawar N100m

'Na So Ya Fi Haka': Tsohon Gwamna Ya Koka kan Tattalin Arziki yayin ba da Gudunmawar N100m

  • Tsohon Gwamnan Delta, James Ibori, ya ba Jami’ar Igbinedion gudunmawar Naira miliyan 100 domin tallafa mata da ci gaban ilimi
  • Ibori ya ce matsin tattalin arziki ne ya hana shi yin abin da ya fi haka don inganta jami’ar a Okada da ke jihar Edo a Kudancin Najeriya
  • Ya yaba da gagarumin aikin Esama Gabriel Igbinedion wajen kafa makarantu daga matakin firamare har zuwa jami’a a Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, ya ba da gagarumar gudunmawa domin tallafawa ilimi.

Ibori ya bayyana cewa matsin tattalin arziki ya hana shi ba da cikakken tallafi ga Jami’ar Igbinedion domin ci gaban ilimi.

Tsohon gwamna ya koka kan matsin tattalin arziki
Tsohon gwamna, James Ibori ya ba da gudunmawa domin tallafawa ilimi. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Tsohon gwamna ya koka kan matsin tattalin arziki

Ibori ya yi wannan bayani ne a wani taro da aka gudanar a Abuja don kaddamar da littafin tarihin Esama na Benin, Gabriel Igbinedion, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Masana'antar fina finan Najeriya ta yi rashi, matashiyar jaruma ta riga mu gidan gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin taron, James Ibori ya sanar da bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 ga jami’ar domin ci gabanta da kuma bunkasa sashen tattalin arziki.

Ibori ya ce:

“Zan ba da gudunmawa kadan don kafa kujera a tsangayar tattalin arziki. Da ba don matsin tattalin arziki ba, zan bayar da yawa.”

Ya kara da cewa gudunmawar da ya bayar ta samo asali ne daga gagarumin tasirin da Esama Igbinedion ya yi a fannin ilimi a Najeriya.

“Zan iya bayar da wannan gudunmawa ne saboda na san aikin Esama zai ci gaba da dorewa har zuwa makoma."

- Cewar James Ibori

Ibori ya ba da gudunmawar N100m don ci gaban ilimi
Tsohon gwamna, Ibori ya nuna damuwa kan matsin tattalin arziki. Hoto: James Ibori.
Source: Facebook

Ibori ya yabawa gudunmawar Igbinedion a fannin ilimi

Ibori ya bayyana Esama a matsayin mutum mai himma da kishin al’umma wanda ya sadaukar da dukiyarsa wajen ci gaban dan Adam.

Ya ce Esama ya kafa makarantar yara, makarantar firamare, sakandare da har ma da jami’a a Najeriya domin inganta rayuwar al’umma.

Kara karanta wannan

Abincin wasu ya ƙare: Bayan ambaliya, Gwamna Zulum ya kori wasu kwamishinoni

“Me kuma mutum zai yi wa al’umma bayan haka?”

Ibori ya tambaya cikin jin dadi da yabo ga jagoran ilimi inda yake bayyana muhimmancin ilimi a cikin al'umma da kuma yadda ke akwo sayui.

Alkawarin da Ibori ya yi wa Lucky Igbinedion

Ibori ya kuma yi alkawarin ci gaba da tallafawa Lucky Igbinedion, wanda ke matsayin mataimakin shugaban jami’ar.

Ya kara da cewa:

“Mai girma mataimakin shugaban jami’a, za ka ci gaba da samun goyon bayana wajen bunkasa wannan makaranta."

Taron ya samu halartar manyan baki da dama wadanda suka yaba da irin gudummawar Ibori da irin gagarumin tarihin Esama a ilimi.

Ibori ya jagoranci gwamnoni zuwa Aso Rock

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi wata ganawa da wasu daga cikin tsofaffin gwamnoni a Najeriya da suka yi mulki bayan dawowa dimokuraɗiyya.

Shugaba Tinubu ya karɓi tsofaffin gwamnonin da suka yi mulki tare a shekarar 1999 a fadar Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja.

Tsohon gwamna, James Ibori ne ya jagoranci tsofaffin gwamnoni, waɗanda suka taka muhimmiyar rawa tun farkon mulkin dimokuradiyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.