Kano: Mata Sun Gaji, Ɗaruruwa Sun Fito Zanga Zanga kan Yawaitar Faɗan Daba
- Mata sun yi zanga-zanga a Kofar Mata domin nuna damuwarsu kan rikice-rikicen ‘yan daba da ke ci gaba da kashe mutane
- Sun bukaci gwamnati da hukumomin tsaro da su gaggauta daukar mataki domin dakile rikice-rikicen da suka yi kamari tsakanin ‘yan daba
- Sun ɗauki matakin fito wa zanga-zanga ne bayan da ƴan daba suka jera kusan kwanaki biyar suna ɗauki ba daɗi ba gaira ba dalili
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kano – Ɗaruruwan mata daga unguwar Kofar Mata da ke cikin karamar hukumar birnin Kano sun fito zanga-zanga a ranar Asabar.
Sun yi fitar ɗango domin nuna fargabarsu da rashin jin daɗi kan yawaitar hare-hare da kisan gilla da ake zargin 'yan daba da aikatawa a sassan jihar.

Source: UGC
Jaridar Leadership ta ruwaito masu zanga-zangar sun hada da iyaye mata da ƴaƴansu mata, inda suka rika yawo a manyan titunan unguwar suna neman a dauki mataki kan daba.
Mata sun yi zanga-zanga a Kano

Kara karanta wannan
Ruwa da iska mai ƙarfi sun kifar da jirgi bayan ya ɗauko fasinjoji a jihar Jigawa
Daily Post ta wallafa cewa matan na dauke da alluna masu rubuce-rubucen kira gwamnatin jihar Kano da hukumomin tsaro da su gaggauta shawo kan matsalar rashin tsaro da ta addabi yankinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Guda daga cikin matan ta ce:
“Wannan abin ya ƙi ci, ya ƙi cinye wa."
"'Yan daba daga Zango da Kofar Mata na ta fafatawa tun sama da sati guda. Lamarin na kara tsanani. Yara biyu sun mutu, wasu da dama sun jikkata. Mun gaji da zama a cikin fargaba."
Mazauna yankin sun bayyana cewa rikicin kan barke ba tare da wata alamar za a samu hatsaniya ba inda ‘yan daba ke kai farmaki ga jama’a tare da fasa shaguna suna fashi.
Daba ta yi ƙamari a jihar Kano
Yankin Kofar Mata ya shahara da yawan rikicin ‘yan daba, wanda ke jawo jikkatawa da rasa rayuka akai-akai.

Source: Facebook
Matan sun bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da hukumomin tsaro da su hanzarta daukar matakin da zai kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Wata da ke zaune a yankin, Ramla Tanko Labaran ta ce:
"Kwanaki ina cikin gida na ji ana hayaniya, kuma nuna kallonsu suna yankar junansu, sai dai ki ga jini."

Kara karanta wannan
An fara zanga zangar fatattakar ƴan Najeriya a Ghana, an faɗi laifuffukan da suke aikatawa
Wata ma'aikaciyar jinya da ta nemi a sakaye sunanta ta shaida wa Legit cewa:
"Na fito daga wajen aiki na wuce wajen ke nan, sai na ji harbe-barbe da borkonon tsohuwa." Kin ji fargabar da na ji? Allah dai ya kyauta."
Matsalar daba ta fara zama ruwan dare a Kano, inda haka kawai sai a ga faɗa ya ɓarke yayin da matasan ke kashe junansu ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba.
An yi sabon zargi kan kwamishinan Kano
A baya, mun wallafa cewa rahoton da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta fitar ya bayyana cewa kwamishinan sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Namadi ya yamutsa hazo.
Rahoton ya ce kwamishinan ya karɓi cin hancin $30,000 daga wani sanannen ɗan safarar miyagun ƙwayoyi, Sukaiman Danwawu, domin ya tsaya masa a kotu.
Ibrahim Namadi na daga cikin majalisar zartarwa ta Kano a karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, kuma yanzu ana binciken sa bisa zargin hannu a belin Ɗanwawu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng