Kungiyar Kare Hakkin Musulmi Ta Miƙa Muhimmiyar Buƙata ga Gwamnatin Tinubu

Kungiyar Kare Hakkin Musulmi Ta Miƙa Muhimmiyar Buƙata ga Gwamnatin Tinubu

  • Kungiyar kare haƙkin muaulmi ta MURIC ta buƙaci gwamnatin tarayya ta kafa kotunan shari'a a duka jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja
  • Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya ce rashin adalci ne kafa kotunan dokar turawa a kowace jiha yayin da Arewa kaɗai ke da kotunan shari'a
  • Ya buƙaci Gwamnatin Tinubu ta tabbatar da adalci ta hanyar samar da kotunan shari'a har a Kudancin ƙasar nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kungiyar kare haƙƙin Musulmi ta Najeriya (MURIC) ta roƙi Gwamnatin Tarayya da ta shigar da kotunan Shari’a cikin tsarin shari’ar ƙasar nan.

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta bayyana cewa tsarin shari’ar Najeriya a yanzu ya nuna son kai ƙarara saboda an hana aiwatar da shari’ar Musulunci a wasu sassa.

Shugaban ƙungiyar MURIC na ƙasa, Farfesa Ishaq Akintola.
MURIC ta bukaci a kafa kotunan shari'ar musulunci a jihohi 36 da Abuja Hoto: @Muslimrights
Source: Twitter

Kamar yadda Premium Times ta rahoto, MURIC ta ce yayin da kotunan dokar ƙasa ke aiki a kowane yanki, bai kamata a hana musulmi damar samun kotunan shari'a ba.

Kara karanta wannan

'Dan Najeriya ya fitar da fassarar Kur'ani irinta ta farko a duniya bayan aikin shekaru 22

MURIC ta aika saƙo ga Gwamnatin Tinubu

Bisa haka ne ƙungiyar ta bukaci Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu da ta ɗauki kotunan Shari’a a matsayin kotunan tarayya.

Haka kuma MURIC ta bukaci gwamnatin ta tabbatar da hakan ta hanyar kafa su a duka jihohi 36 da Abuja kamar yadda aka kafa kotun tarayya kowane jiha.

Wannan kira ya fito ne a ranar Jumma’a, 1 ga Agusta, 2025, daga hannun shugaban ƙungiyar MURIC na ƙasa, Farfesa Ishaq Akintola.

Meyasa babu kotunan shari'a a Kudu?

A rahoton Vanguard, Farfesa Akintola ya ce:

"Al'ummar musulmi na kara nuna damuwa kan batun kotunan shari'a. Ɗaya daga cikin tambayoyin da aka dade ana yi shine, meyasa Gwamnatin Tarayya ta kafa kotun tarayya a kowace jiha duk da cewa akwai kotunan jihohi?
"Kuma kowa ya sani cewa akwai kotunan jiha da tarayya a kowace jiha, alhali kotunan Shari’ar musulunci suna aiki ne kawai a Arewa. Babu ko guda ɗaya a Kudu."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jihar Neja ta maka gwamnatin Tinubu kara gaban Kotun Koli

"Wannan yana nuna cewa, duk da Musulmin Najeriya sun amince kotunan Turawa da suka samo asali daga Kiristanci, Kiristocin Najeriya kuma ba su yarda da kotunan Shari’a ba."
Shugaban MURIC da Bola Ahmed Tinubu.
MURIC ta buƙaci gwamnati ta yiwa musulmi adalci a jihohin Najeriya Hoto: @muslimrights, @OfficialABAT
Source: Twitter

Ƙungiyar musulunci ta bayar da mafita

Shugaban MURIC ya kara da cewa hakan ya nuna cewa an take wa musulmi haƙƙinsu na samun kotunan shari'a a Kudu, yayin da Kiristoci ke samun yadda suke so.

Ishaq Akintola ya buƙaci gwamnatin Tinubu ta duba wannan lamari, ta tabbatar da ƴancin musulmi na samun kotun shari'a a ko'ina a faɗin ƙasar nan.

"Gwamnatin Tarayya ce ya kamata ta tabbatar ba a tauye haƙƙin Musulmi ba, ta hanyar gujewa nunawa shari’a wariya ko kabilanci ba," in ji shi.

MURIC ta caccaki Jami'ar Adeleke

A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar MURIC ta zargi jami’ar Adeleke da hana dalibai Musulmi gudanar da ibadun watan azumin Ramadan.

Babban daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya ƙara da cewa jami’ar ta na tilasta wa dalibai Musulmi halartar shirye-shiryen cocin jami’ar.

Ya ce jami’ar na amfani da hanyoyi daban-daban don hana dalibai Musulmi gudanar da addininsu na musulunci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262