Mahaifin Yarinyar da Malamin Musulunci Ya Kashe Ya Roki Gwamnan Kwara Alfarma
- Mahaifin Hafsoh Yetunde Lawal ya roƙi Gwamnan Kwara ya sanya hannu kan hukuncin ratayar malamin da ya kashe diyarsa
- Kotun Kwara ta yanke wa Abdulrahman Bello hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kisan ɗalibar Kwaleji, Hafsoh Yetunde Lawal
- Lauyoyi da ƙungiyar IEDPU sun nemi gwamnati ta hanzarta aiwatar da hukuncin kisan domin nuna cewa doka tana aiki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - An yankewa wani malamin addinin Musulunci, Abdulrahman Bello hukuncin kisa ta hanyar rataya daga kotun jihar Kwara.
Ana zargin malamin ne bisa laifin kashe Hafsoh Yetunde Lawal, wata dalibar Kwalejin Ilimi da ke jihar.

Source: Twitter
Mahaifin Hafsoh ya yabawa jami'an tsaro
Mahaifin yarinyar, Ibrahim Lawal Adifalu yayin wata hira da wakilin Legit.ng ya roki alfarma wurin gwamnan jihar Kwara.
Hakan na zuwa ne bayan kotun koli da ke Ilorin ta tabbatar da cewa Abdulrahman ya aikata laifin kisan gilla, sannan ta sallami sauran mutum huɗu da ake tuhuma tare da shi.
Bayan yanke hukuncin, mahaifin marigayiya Hafsoh, Ibrahim Lawal Adifalu, ya nuna godiya ga gwamnati da jami’an tsaro da kuma kotun da DSS.
Adifalu ya ce idan ba don binciken DSS ba, da ba za a samu cikakken shaidar da ta tabbatar da laifin ba.
Abin da mahaifin Hafsoh ke rokon gwamna
Ya ce hukuncin kotu ya nuna cewa adalci yana yiwuwa idan hukumomi suka yi aiki tare da gaskiya da natsuwa.
Sai dai ya nemi Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da ka da ya yi jinkiri, ya sa hannu kan takardar hukuncin nan da wuri.
A cewarsa, gwamnati ta taka rawar gani wurin ganin an samu wannan hukunci, don haka ya kamata ta kammala aikin da ta fara.

Kara karanta wannan
Bayan Muhuyi ya sauka, Gwamna Abba ya naɗa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano

Source: Original
An bukaci gaggawar aiwatar da hukuncin kisa
Wani lauya daga jihar Kwara, Attairu Haruna Galad, ya ce aiwatar da hukuncin shi ne zai tabbatar da adalci da kawo karshen irin wannan laifi.
Ya ce ba daidai ba ne a rika ciyar da masu laifi a gidan gyaran hali da kudin haraji yayin da iyalan mamata ke fama da baƙin ciki.
Kungiyar 'Ilorin Emirate Descendants Progressive Union' (IEDPU) ta bayyana goyon bayanta ga hukuncin kisan da aka yanke.
Ta ce aiwatar da hukuncin cikin gaggawa zai zama darasi ga masu niyyar aikata laifuffukan asiri da kisa.
Kungiyar ta jinjina wa gwamnatin jihar, kotun da jami’an tsaro bisa kokarinsu wajen tabbatar da adalci a wannan shari’ar.
Kotu ta tura malamar Musulunci gidan kaso
Mun ba ku labarin cewa an tura wata shahararriyar malamar addinin Musulunci daga Ibadan, Alhaja Kafilat Kaola gidan gyaran hali na Oke Kura a Ilorin, Jihar Kwara.
Kaola na fuskantar tuhuma kan batanci da take yi wa wani malami, Alhaji Taofeek Akeugbagold, inda ta ce shi boka ne kuma mutane su guje shi.
Lauyan Akeugbagold ya gabatar da bidiyo inda Kaola ke zagin alkalai, don haka kotu ta ki bayar da beli, ta tura ta kurkuku har 17 ga Yulin 2025 da ta gabata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

