Abin da Doka Ta Tanada kan Ayyana Zaben Kano na 2019 da Wasu Zaɓuka da 'Inconlusive'

Abin da Doka Ta Tanada kan Ayyana Zaben Kano na 2019 da Wasu Zaɓuka da 'Inconlusive'

  • A zaɓukan da suka gabata a Najeriya, an sha ayyana wasu daga ciki a matsayin ba su kammalu ba watau 'inconclusive'
  • Zaɓen gwamnan jihar Kano na shekarar 2019 na daga cikin wanda aka kira da wannan kalma kafin daga bisani a bayyana wanda ya yi nasara
  • Kwamishinan zaɓen Kano, Abdu Zango ya nuna cewa wannan kalma ta inconclusice babu ita a kundin dokokin zaɓen Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Kwamishinan Zaɓe (REC) na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a Jihar Kano, Abdu Zango, ya yi ƙarin haske kan ayyana zaɓe a matsayin wanda bai kammalu ba.

Kwamishinan INEC mai kula da harkokin zaɓe a Kano, Abdu Zango ya bayyana cewa dokar zaɓe ta Najeriya ba ta san kalmar “zaɓen da bai kammalu ba," ma'ana inconclusive.

Kara karanta wannan

Bayan Muhuyi ya sauka, Gwamna Abba ya naɗa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano

Babu dokar da ta ambaci kalmar inconclusive.
Kwamishinan zaɓen Kano ya yi bayani kan ayyana zabe da wanda bai kammalu ba Hoto: @INECNigeria
Source: Twitter

Kano haɗu da Inconclusive a zaɓen 2019

Daily Trust ta tattaro cewa a Najeriya, ana yawan jin cewa an bayyana zaɓe da cewa bai kammalu ba idan yawan ƙuri’un da aka soke ya fi tazarar da ke tsakanin 'yan takarar da ke kan gaba.

Misali, a zaɓen gwamnan Kano na 2019, an ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammalu ba, inda daga bisani aka shirya sabon zaɓe a wasu mazaɓu kafin a sanar da wanda ya yi nasara.

Sai dai a ranar Alhamis, 31 ga watan Yuli, 2025, kwamishinan INEC na Kano ya ce dokar zaɓen Najeriya ba ta san kalmar Inconclusive ba.

Abdu Zango ya faɗi haka ne a wurin taron masu ruwa da tsaki kan harkokin zaɓe a hedikwatar hukumar INEC da ke Kano.

An shirya wannan taro ne kan batun zaɓen cike gurbi da za a gudanar a ranar 16 ga watan Agusta a mazabun Bagwai/Shanono da Ghari/Tsanyawa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da kashe sama da N712bn a yi wa filin jirgin Legas kwaskwarima

Menene hukuncin kalmar inconlusive a doka?

Kwamishinan zaɓen ya jaddada cewa babu wata doka a kundin dokokin zaɓen Najeriya da ta ambaci kalmar “inconclusive” watau zaɓen da bai kammalu ba.

“Inconclusive kalma ce da ba ta da gurbi a cikin dokar zaɓen Najeriya. Doka ba ta san da ita ba.
"Wannan ne ya sa a lokacin zaɓen 2023, na sanar da cewa za mu gudanar da zaɓe kuma mu bayyana wanda ya yi nasara ba tare da amfani da kalmar inconclusive ba.

- Abdu Zango.

Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmud Yakubu.
Dokar zaben Najeriya ba ta san kalmar 'zaben da bai kammalu ba' Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Za a yi zaɓen cike gurbi a mazaɓun Kano 2

Ya bayyana cewa zaɓen cike gurbi a mazabar Bagwai/Shanono za a gudanar da shi ne saboda rasuwar ɗan majalisar da ke kan kujerar.

A cewarsa, za a ƙarasa zaɓe a rumfunan zaɓe guda 10 a yankin Ghari na ƙaramar hukumar Ghari/Tsanyawa bisa umarnin kotu.

INEC ta kara karɓar takardun neman rijista

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zaɓen Najeriya watau INEC ta bayyana cewa adadin ƙungiyoyin da suka nemi zama jam'iyyu sun kai 144.

Kara karanta wannan

"Babu mai dakatar da mu," An shirya kawo wa Tinubu, APC miliyoyin ƙuri'u a Kano a 2027

Adadin ya ƙaru ne bayan INEC ta tabbatar da karɓar ƙarin takardun neman zama jam'iyyun siyasa daga wasu ƙungiyoyi 10.

Hukumar INEC ta ce a halin yanzu tana nazarin takardun neman rajista da ta karɓa don tantance wacce kungiya ta cika sharuddan da za ta iya neman zama jam'iyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262