Damfara: Rundunar Ƴan Sanda Ta Kama Matashi da ke Kwaikwayon Muryar Gwamnoni

Damfara: Rundunar Ƴan Sanda Ta Kama Matashi da ke Kwaikwayon Muryar Gwamnoni

  • ‘Yan sanda sun kama matashi a Kaduna da ake zargi da kwaikwayon muryoyin gwamnoni domin damfarar bayin Allah
  • Kakakin rundunar, ASP Mansur Hassan ya tabbatar da kamen, inda ya ce Allah Ya yi wa matashin baiwar satar muryoyin jama'a
  • ASP Mansur Hassan ya ƙara da cewa an samu matashin da lambobin wayar manyan mutane da ya damfara a ƙasar nan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama wani matashi da ake zargi da amfani da fasahar kwaikwayon muryoyin wasu gwamnoni da manyan mutane.

Rundunar ta bayyana takaici a kan yadda matashin, wanda ba a bayyana sunansa ba ya rika amfani da baiwarsa wajen damfarar jama’a da kuɗi masu yawa.

Kara karanta wannan

Masana'antar fina finan Najeriya ta yi rashi, matashiyar jaruma ta riga mu gidan gaskiya

Yan sanda sun yi kame a Kaduna
Rundunar yan sanda ta kama ɗan damfara a Kaduna Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Kakakin rundunar, ASP Mansur Hassan, ya shaida wa BBC Hausa cewa rundunar ta jima tana neman matashin.

Ƴan sanda sun yi ram da matashi

Daily Post ta ruwaito rundunar ta kara da cewa an samu korafe-korafe a kan yadda matashin ya riƙa damfarar wasu manya a Najeriya da sunan wasu gwamnonin Arewa.

ASP Mansur Hassan ya ce:

"Bayan kama shi mun same shi da lambobin waya da dama daga cki har da na manyan mutane a ƙasar nan."
"Mutumin ya ƙware sosai wajen kwaikwayon muryoyin mutane, duk wani mutum da ba ka tunani zai iya yi maka muryarsa."

Ra’ayoyin jama’a kan kama matashin a Kaduna

Kama matashin ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin rundunar ‘yan sanda ta fi saurin kama masu kananan laifuffuka.

Jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya
Yan sanda sun kama mai kwaiwayon muryar gwamnonin Arewa Hoton: Nigeria Police Force
Source: UGC

@realadnantweet ya ce:

"Amma me yasa hanzu suka kasa kama Bello Turji da Alero?"

Kara karanta wannan

Motar sojojin Najeriya ta fada babban rami a mummunan hadari, an rasa rai

@Dan_Malama_05 Sa’id ya rubuta:

"Tofa talakawa mun ga ta kanmu."

@matar_mijintaa ta wallafa:

"A nan kuka kware, amma baku iya kama 'yan ta'adda ba wanda ake lives da su a social media, kun kasa kamasu. Allah ya kyauta."

@Byaubash ya ce:

"Iya jarumtar su kenan."

Matashin, wanda ba a bayyana sunansa ba tukuna, yana hannun ‘yan sanda kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano yawan waɗanda ya yaudara da kuma irin kuɗin da ya karɓa.

Rundunar ba ta sanar da sunaye ko adadin kuɗin da ake zargin matashin da sata daga hannun mutanen da ya yaudara.

Gwamnan Kaduna ya magantu kan biyan fansa

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin jihar Kaduna ta karyata zargin da ake dade ana yadawa cewa tana biyan ‘yan ta’adda kudin fansa domin su saki mutanen da suka sace.

Gwamnan jihar, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa bai taba biyan ko sisin kwabo ga masu tada zaune tsaye ba tun lokacin da ya hau kan mulki da sunan tabbatar da zaman lafiya.

Uba Sani ya jaddada cewa gwamnatin sa na aiki tukuru wajen tallafawa wadanda rikicin ya rutsa da su, ba wai sasanta wa da mutanen da ke gallaza wa talakawansa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng