Motar Sojojin Najeriya Ta Fada Babban Rami a Mummunan Hadari, An Rasa Rai

Motar Sojojin Najeriya Ta Fada Babban Rami a Mummunan Hadari, An Rasa Rai

  • Wani sojan rundunar Operation Hadin Kai ya rasu a mummunan haɗarin mota da ya faru kusa da Damagum a jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas
  • Rahotanni sun nuna cewa haɗarin ya faru ne yayin da sojoji ke tafiya a kan hanyar Jos/Damaturu domin wani aiki na musamman
  • Motar ta faɗa rami ne bayan direban ya rasa ikon tafiyar da ita kuma hakan ya jawo mika wani jami'in soji asibitin Damagun da ke kusa da wajen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Yobe – Wani soja da ke aiki a ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai ya rasa ransa, yayin da wasu biyu suka jikkata a wani mummunan haɗarin mota da ya shafi wata motar soji.

Rahotanni da Legit Hausa ta samu sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da sojojin ke kan hanyar Damaturu/Jos, a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Damfara: Rundunar ƴan sanda ta kama matashi da ke kwaikwayon muryar gwamnoni

Motar sojojin Najeriya ta yi hadari a Yobe
Motar sojojin Najeriya ta yi hadari a Yobe. Hoto: Zagazola Makama
Asali: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na yamma a ranar Alhamis, 31 ga watan Yuli, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu rahotanni sun bayyana cewa an yi hadarin ne kusa da unguwar Garri Tasha a yankin Damagum da ke Ƙaramar Hukumar Fune.

Motar sojoji ta faɗa rami mai zurfi

Wata majiya da ta tabbatar faruwar lamarin, ta ce motar sojin ta taso ne daga hedikwatar soji da ke Damaturu, tana dauke da wasu jami'an tsaro da ke kan aiki na musamman.

Majiyar ta ce yayin tafiyar, direban motar ya rasa iko da tafiyar da ita, lamarin da ya sa motar ta faɗa wani rami mai zurfi da ke gefen hanya.

An garzaya da waɗanda suka jikkata asibiti

Ma’aikatan ceto a Damagum sun isa wurin cikin gaggawa inda suka taimaka wajen ceto sojoji biyu da suka jikkata sosai a sakamakon haɗarin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da kashe sama da N712bn a yi wa filin jirgin Legas kwaskwarima

Rahoton ya bayyana cewa an garzaya da su zuwa Asibitin Gwamnati na Damagum domin kula da lafiyarsu.

Daya daga cikinsu, wanda aka gano da suna Sajan Salami Ahmed, an tura shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Yobe da ke Damaturu domin samun cikakken kulawa.

Hafsun tsaron Najeriya, Christopher Musa
Hafsun tsaron Najeriya, Christopher Musa. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

An tabbatar da mutuwar soja 1

A cewar majiyar, daya daga cikin sojojin da hadarin ya rutsa da su ya rasu nan take a wajen haɗarin.

Gawarsa ta kasance a wurin har sai da aka zo aka kwashe ta, inda daga bisani aka mika shi ga kwamandan rundunarsa domin aiwatar da matakan da suka dace.

Najeriya kasa ce da ake yawan fama da haduran mota musamman a manyan tituna tsawon shekaru da suka gabata.

Sojoji sun hallaka 'Dan Dari Biyar'

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun hallaka gawurtaccen dan bindiga da ake kira da Dan Dari Biyar.

Kara karanta wannan

An yi rashi, tsohon dan majalisa ya bar duniya a dalilin mummunan hatsarin mota

Rahotanni sun bayyana cewa dan bindigar na cikin manyan 'yan ta'addan da suka addabi al'umma a jihar Sokoto.

Legit ta gano cewa Dan Dari Biyar ya shahara da karbar kudin fansa, baya ga haka kuma yana azabtar da wadanda ya sace.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng