Bayan Muhuyi Ya Sauka, Gwamna Abba Ya Naɗa Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci Ta Kano

Bayan Muhuyi Ya Sauka, Gwamna Abba Ya Naɗa Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci Ta Kano

  • Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya sauka daga shugabancin hukumar PCACC ta Kano bayan karewar wa'adinsa
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jinjina masa bisa ayyukan da ya yiwa Kano, ya ce ƙofarsa a buɗe take don sake aiki da shi nan gaba
  • Abba ya kuma tura sunan wanda zai maye gurbinsa ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin tantancewa da tabbatar da naɗinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa sabon shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙirafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC).

Gwamna Abba ya aika sunan Saidu Yahya zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano domin tantancewa da tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban hukumar PCACC.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.
Muhuyi Magaji Rimin Gado ya sauka daga matsayin shugaban hukumar PCACC ta Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da kashe sama da N712bn a yi wa filin jirgin Legas kwaskwarima

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Muhuyi ya suka daga muƙamin?

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wannan mataki ya zo ne bayan saukar Muhuyi Magaji Rimingado, wanda wa’adinsa ya ƙare a baya-bayan nan.

A ranar Litinin da ta gabata, hukumar PCACC ta fitar da wata takarda ta nada Zahraddeen Kofar Mata a matsayin Shugaban riko na hukumar.

Wannan lamarin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ma’aikata da masu ruwa da tsaki daga ciki da wajen hukumar.

Gwmana Abba ya maye gurbin Muhuyi Magaji

Sai dai a sanarwar da Sanusi Dawakin Tofa ya fitar, ya ce wanda gwamna ya naɗa, Saidu Yahya, kwararre ne a fannin yaƙi da cin hanci kuma gogaggen jami'in gwamnati.

An haifi Yahya a 1978 kenan yana da shekaru 47 a duniya. Ya samu digiri na farko a fannin tattalin arziki daga Jami’ar Bayero Kano (BUK) da kuma digiri na biyu (MBA) a Gudanar da Kasuwanci.

Saidu Yahya ya samu ƙwarewa mai tarin yawa daga Hukumar ICPC, inda ya rike muƙamai masu mahimmanci.

Kara karanta wannan

Shirin kayar da Tinubu ya kankama, an bayyana wanda zai iya gyara Najeriya a 2027

Gogewar sabon shugaban PCACC ta Kano

Kafin a miƙa sunansa don tantancewa, shi ne shugaban ƙungiyar bincike na Musamman da bibiya kan ayyukan Majalisa da manyan jami’an gwamnati, kuma mamba ne a Kwamitin Ayyuka na ICPC.

Yana gogewar aiki ta shekaru fiye da 18 a fannin binciken laifuffukan cin hanci da rashawa, sannan masani ne wajen koyar da dabarun bincike da sa ido kan aiwatar da ayyuka.

Sanarwar ta ce ana sa ran ƙwarewarsa a fannin bincike da bin sawun dukiyoyi za ta ƙara wa hukumar PCACC ƙarfin wajen yaƙi da cin hanci a jihar Kano.

Har ila yau, Gwamna Abba ya amince da nadin Barista Hafsat Ada'u Kutama a matsayin sabuwar sakatariya kuma mai ba da shawara kan harkokin shari’a a hukumar PCACC.

Gwamna Abba da Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Gwamna Abba ya sanar da naɗin Sa'idu Yahya a matsayin sabon shugaban PCACC Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Gwamna Abba ya yabawa Muhuyi Magaji

Ya kuma ba da umarnin mayar da tsohon sakataren hukumar, Barista Zaharadden Hamisu Kofar Mata, zuwa Ma’aikatar Shari’a domin a sake tura shi wani aiki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga ganawa da ministoci da manyan ƙusoshin gwamnati a Aso Rock Villa

Gwamna ya yaba wa tsohon Shugaban Hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, bisa jajircewarsa, dauriya, sadaukarwa da hidimar da ya yiwa Jihar Kano.

"Ƙofar Gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da zama a buɗe domin yin aiki da Barista Muhuyi a nan gaba, idan damar hakan ta taso,” inji Gwamna Abba.

Gwamnatin Kano ta gyara makarantu 1,200

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta bayyana cewa ta kammala gyaran makarantu sama da 1,200 a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Kwamishinan ilimi na Kano, Dr. Ali Haruna Makoda ya bayyana cewa wannan wani ɓangare ne na matakan da gwamnati ke ɗauka domin farfaɗo da harkar ilimi.

Ya ƙara da cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya kuma ware Naira biliyan 3 domin gyara makarantu 13 na ‘yan mata, wanda aka rufa a baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262