Gwamnatin Tinubu Ta Fito da Shirin Tallafawa Mutane Miliyan 8 a Fadin Najeriya

Gwamnatin Tinubu Ta Fito da Shirin Tallafawa Mutane Miliyan 8 a Fadin Najeriya

  • Gwamnatin tarayya za ta tallafa wa sama da mutane miliyan 8.8 a cikin gundumomi 8,809 na ƙasar nan
  • Shirin zai taimaka wa matasa 1,000 zuwa 2,000 a kowace gunduma domin ƙarfafa sana’o’i da rage talauci
  • Za a gudanar da shirin ne a haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi domin habaka tattali

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sabon shirin farfaɗo da tattali a matakin gunduma mai suna RHWDP.

Rahotanni sun nuna cewa shirin na da nufin tallafa wa sama da mutane miliyan 8.8 a faɗin ƙasar nan.

Gwamnatin tarayya ta kawo shirin tallafawa al'umma
Gwamnatin tarayya ta kawo shirin tallafawa al'umma. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A sakon da Bayo Onanuga ya wallafa a X, Legit ta gano cewa an bayyana shirin ne a ranar Alhamis yayin taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC) karo na 150.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da kashe sama da N712bn a yi wa filin jirgin Legas kwaskwarima

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ministoci sun amince da fara aiwatar da shirin a dukkan gundumomi 8,809 na Najeriya.

Yadda za a tallafawa matasan Najeriya

Ministan Kasafin Kuɗi, Atiku Bagudu, ya gabatar da shirin a gaban shugabannin ƙasa, inda ya bayyana cewa RHWDP na da nufin samar da ci gaba kai tsaye a ƙananan hukumomi.

Bagudu ya bayyana cewa shirin na da nufin rage talauci, haɓaka noma, ƙirƙirar ayyukan yi da kuma samar da kwanciyar hankali ga al’umma.

“Mun tsaida kuduri cewa kowace gunduma za a zaɓi akalla mutane 1,000 zuwa 2,000 lura da girman gundumar. Za a ba su tallafi domin su yi sana’a da habaka tattalin arzikin yankinsu,”

- Inji Bagudu.

Ya ce shirin yana da asali a kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da ke buƙatar gwamnati ta tabbatar da wadatar abinci da ci gaba a yankuna.

Ministan kasafi tare da shugaba Bola Tinubu
Ministan kasafi tare da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Za a yi haɗin gwiwa a matakai daban-daban

Kara karanta wannan

Gingima gingiman bashi 6 da Bola Tinubu ya ci daga fara mulkin Najeriya

Bagudu ya bayyana cewa wannan shiri zai kasance aikin haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

A 2023 aka nada Bagudu a matsayin ministan kasafi da tsare-tsaren tattali, watanni bayan ya gama mulkin jihar Kebbi na tsawon shekaru takwas.

Arise News ta rahoto ya ce an kafa kwamitin jagoranci na ƙasa da wakilai daga kowane yanki na ƙasar nan don sa ido a kan yadda za a gudanar da shirin.

Shirin HWDP na cikin manufofin bunkasa tattali

Gwamnatin tarayya ta ce shirin RHWDP na daga cikin matakan da za su taimaka wajen cimma burin tattalin arzikin Dala tiriliyan 1 da gwamnatin Tinubu ke fatan samu kafin 2030.

Hakan na zuwa ne yayin da ake buƙatar haɓakar tattalin arziki zuwa kaso 15 cikin ɗari, daga kasa da kaso 4 da ake ciki yanzu.

Bagudu ya ce shirin ya samu karɓuwa daga rahoton Majalisar Kuɗin Duniya (IMF), wadda ta yaba da matakan sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnati ke aiwatarwa.

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, wanda ya halarci taron, ya yaba da ƙoƙarin shugaba Tinubu wajen samar da ƙarin kuɗin shiga ga ƙasa.

Kara karanta wannan

An yi hasashen yawan ƙuri'un da Shugaba Tinubu zai samu a zaɓen 2027

Amma duk da haka ya ce:

“Kalubalen yanzu shi ne yadda wannan kuɗi zai shafi rayuwar al’umma kai tsaye.”

Ayyukan Tinubu za su samar da aikin yi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta sanar da shirin samar da jiragen kasa a jihohin Arewa.

Ministan sufuri, Sanata Sa'idu Alkali ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen samar da sana'o'i 250,000.

Sanata Sa'idu Alkali ya bayyana cewa ana hasashen duk wanda ya samu aikin yi a sanadiyyar ayyukan zai samu albashi N150,000 a wata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng