Tinubu Ya Amince da Kashe sama da N712bn A Yi wa Filin Jirgin Legas Kwaskwarima
- Gwamnati za ta kashe N712.26bn wajen ayyukan filin jirgin saman Legas domin zamanantar da ita
- Majalisar zartarwa ta amince da kashe kudin don gina sabon tsarin lantarki, da sauran kayayyakin zamani
- Sauran ayyukan sun haɗa da sake fasalin wuraren ajiye jirage a tashar jirgin da tabbatar da tsaron jama'a
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) ta amince da yi wa wani ɓangare na filin jirgin saman Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas Kwaskwarima.
An yanke wannan hukunci ne a zaman FEC da aka gudanar a ranar Alhamis, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja

Source: Facebook
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa wannan mataki na cikin babban shirin gyaran ababen more rayuwa a sashen sufurin jiragen sama na Najeriya, wanda ya kai kimanin Naira biliyan 900.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a gyara, sabunta filin jirgin Legas
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana cewa an ba kamfanin China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC) kwangilar aikin.
Ministan ya bayyana cewa aikin zai haɗa da sauya tsofaffin kayan aikin saukar jirage da sanya sababbin na'urorin zamani da suka dace da bukatun yau.
Keyamo ya kara da cewa gwamnatin Tinubu za ta daina gyare-gyaren yau da gobe domin ta mayar da hankali kan warware matsaloli na dogon zango.
Ya tabbatar da cewa aikin zai ɗauki watanni 22, kuma za a biya shi kuɗin gaba ɗaya daga asusun gwamnati kan ayyuka.
Aikin filin jirgin Legas zai laƙume N712.26bn
Jimillar kuɗin aikin da ya shafi filin jirgin saman Legas kaɗai ya kai Naira biliyan 712.26, wanda hakan ke sanya shi cikin manyan ayyuka a tarihin filin jirgin saman Najeriya.
Domin ƙara tsaro a filin jirgin, majalisar ta amince da kashe Naira biliyan 49.9 don gina sabon katanga da za ta kewaya mai nisan kilomita 14.6.

Source: Facebook
Za a haɗa katangar da na’urar CCTV, fitilun rana, titin sintiri da cibiyar sa ido ta zamani da ke aiki yadda ya kamata.
A cewar Keyamo:
"Duk wani abu ko mutum da ya kusanci katangar, za a gano shi nan take tare da sanin wurin da ya ke."
Majalisar ta kuma amince da wasu muhimman ayyukan gyara a manyan filayen jiragen saman ƙasa da ƙasa, ciki har da filin jirgin Malam Aminu Kano da ke Kano.
An ƙera jirgi a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa hukumar Kayan Fasaha da Kere-kere ta Najeriya ta ce aikin kera jirgin sama na farko da aka fara a cikin gida ya kusa zuwa karshe.
Injiniya Kareem Aduagba, wanda ke jagorantar aikin, ne ya bayyana halin da ake ciki a yayin wani taron da hukumar NASENI ta shirya a jihar Kaduna.
Aikin jirgin saman na daya daga cikin manyan nasarori da ake fatan cimmawa a kokarin Najeriya na habaka fasaha da kere-kere a cikin gida Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

