Lokaci Ya Yi: An Shiga Jimami bayan Sarkin Gudi Ya Yi Bankwana da Duniya

Lokaci Ya Yi: An Shiga Jimami bayan Sarkin Gudi Ya Yi Bankwana da Duniya

  • An yi rashi na daya daga cikin sarakunan da ake ji da su a jihar Yobe da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Mai martaba Sarkin Gudi, Alhaji Isa Bunuwo Ibn Madubu Khaji ya yi bankwana da duniya bayan ya kwashe dogon lokaci yana jinya
  • Marigayin wanda aka bayyana a matsayin mai son zaman lafiya ya rasu ne a wani asibiti da ke birnim tarayya Abuja

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Sarkin Gudi, Alhaji Isa Bunuwo Ibn Madubu Khaji, ya yi bankwana da duniya.

Alhaji Isa Bunuwo Ibn Madubu Khaji ya rasu ne bayan ya yi doguwar jinya.

Sarkin Gudi ya rasu a Abuja
Sarkin Gudi ya yi bankwana da duniya Hoto: Imamdeen Hassan Jr.
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ce sanarwar rasuwar sarkin na cikin wata takarda da sakataren masarautar ya fitar, inda aka bayyana cewa Alhaji Isa Bunuwo ya rasu ne a ranar Alhamis a Asibitin Nizamiye da ke Abuja.

Kara karanta wannan

An yi rashi, tsohon dan majalisa ya bar duniya a dalilin mummunan hatsarin mota

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Gudi a jihar Yobe ya rasu

Marigayi sarkin, wanda ke zaune a Gadaka, karamar hukumar Fika ta jihar Yobe, ya rasu bayan ya kwashe wani lokaci yana fama da rashin lafiya, rahoton Daily Post ya tabbatar.

A cewar sakataren masarautar, an shirya gudanar da sallar jana'izar marigayi sarkin a gobe Juma’a da ƙarfe 2:00 na rana a fadar sarkin da ke Gadaka.

Labarin rasuwar sarkin ya girgiza al’ummar yankin, inda da dama ke nuna alhini da yaba masa bisa jagorancinsa da irin tarihi mai kyau da ya bari.

Saƙonnin ta’aziyya daga sassa daban-daban na ƙasar nan na ta shigowa, yayin da mutane ke alhinin wannan babban rashi mai girma.

Wani jigo a jam’iyyar APC, Ibrahim Mohammed Jirgi, ya bayyana marigayi sarkin a matsayin shugaba mai son zaman lafiya wanda ya sadaukar da rayuwarsa don ci gaban majalisar masarautar Gudi da jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan barkewar rikicin kabilanci a Abuja, an tafka barna

Ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin babban rashi ga masarautar Gadaka, yana mai cewa gudunmawarsa ta zarce iyakokin masarautarsa, inda ta shafi rayuwar al’ummarsa, abokansa da masu hulɗa da shi.

"Ina tare da ‘yan masarautarsa wajen jimamin wannan rashi mai girma, kuma muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa da gwamnatin Jihar Yobe.
"Ina roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya jikansa, Ya gafarta masa, Ya yafe kura-kuransa, Ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus."

- Ibrahim Mohammed Jirgi

Sarkin Gudi a jihar Yobe ya rasu
Sarki Gudi ya yi bankwana da duniya Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Karanta wasu labaran kan rashe-rashe

Tsohon gwamnan Kwara ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kwara, Cornelius Olatunji Adebayo, ya koma ga mahaliccinsa.

Kara karanta wannan

Mabambantan ra'ayoyi daga malaman Musulunci game da yafewa marigayi Buhari

Marigayin wanda ya taba rike mukamin minista kuma tsohon sanata ne ya rasu ne yana da shekara 84 a duniya.

Tsohon gwamnan ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da suka yi gwagwarmayar dimokuraɗiyya a ƙarƙashin ƙungiyar NADECO.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel