Gwamnati Za Ta Caje Ɗalibai, Za a Fara Yi Masu Gwajin Ƙwaya
- Ministan ilimi, Tunji Alausa ya ce dole ne a fara aiwatar da gwajin kwaya a manyan makarantu don dakile shan miyagun kwayoyi
- Ya faɗi haka a ganawarsa da da shugaban NDLEA, Buba Marwa mai ritaya, inda suka tattauna hana shan kwaya a makarantu
- Dr. Alausa ya amince a saka darussa na musamman da ke ilmantar da dalibai kan hadurran kwaya a makarantun sakandare
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya goyi bayan fara gwajin kwaya na dole ga daliban makarantun gaba da sakandare a fadin kasar nan.
Wannan mataki ya biyo bayan wata ganawa da ya yi da Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya a Abuja ranar Laraba.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin dakile yawan shan kwaya da ta’ammali da miyagun abubuwa tsakanin dalibai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a fara yi wa dalibai gwajin kwarya
The Guardian ta ruwaito cewa a wata sanarwa da mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar Alausa ya amince a sanya darussa kan illar kwaya a cikin tsarin karatun sakandare.
An kuma amince da haɗin gwiwa a tsakanin ma’aikatar ilimi da NDLEA domin tsara hanyoyin yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi.

Asali: Facebook
Sanarwar da Babafemi ya fitar ta kara da bayyana cewa Marwa ya gabatar da tsari mai matakai uku.
Sun haɗa da: Sake duba darussan da ke koyar da illar kwaya a makarantu, kafa shirin dakile shan kwaya kai tsaye a makarantun sakandare, da kafa dokar gwajin kwaya a jami’o’i da sauran manyan makarantu.
Yawan ta’amalli da kwaya ya fusata NDLEA
Shugaban NDLEA, Marwa, ya bayyana matsalar shan kwaya a matsayin barazana ga tsaron kasa da makomar matasa, yana danganta ta da aikata miyagun laifuka kamar ta’addanci da fashi da makami.
Ya ce:
“Mun dauki wannan yaki ne domin ceton rayukan ’ya’yanmu. Da ba a amfani da kwaya, da dama daga cikin laifuffukan da ake aikatawa ba za su yiwu ba.”
Ya bayyana cewa hukumar ta kama sama da mutane 40,000 da suka aikata laifuffukan kwaya tare da kwace fiye da tan 5,500 na miyagun kwayoyi a shekaru biyu.
“Za mu yi gwajin kwaya a jami’o’i” - Minista
Ministan ilimi, Alausa ya nuna damuwarsa kan yadda yawan matasa ke fadawa cikin shaye-shaye, yana mai cewa:
"Idan matasa na shaye-shaye, ba za su rika zuwa makaranta ba, kuma ko sun je makaranta, ba za su samu ilimi mai amfani ba. A karshe kuma, kaifin tunaninsu zai ragu.”
Ya bayyana cewa gwamnati za ta fara aiwatar da gwajin kwaya ga sababbin dalibai da kuma wadanda suka dawo makaranta.
Hukumar NDLEA ta yi babban kamu
A wani labarin, kun ji hukumar NDLEA ta tabbatar da kama wani fitaccen mutum da ake zargi da safarar kwaya a jihar Kano, Sulaiman Danwawu.

Kara karanta wannan
Noma: Hadimin Buhari ya goyi bayan Tinubu, ya fadi kuskuren da aka samu a zamaninsu
Tun a ranar 10 ga watan Mayu, 2025 rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cafke Danwawu tare da wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.
Bayan haka, an miƙa shi ga hukumar NDLEA domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng