Abincin Wasu Ya Ƙare: Bayan Ambaliya, Gwamna Zulum Ya Kori Wasu Kwamishinoni

Abincin Wasu Ya Ƙare: Bayan Ambaliya, Gwamna Zulum Ya Kori Wasu Kwamishinoni

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi garambawul a gwamnatinsa domin kawo sauyi a cikinta
  • Zulum ya sallami kwamishinoni biyu don farfado da shugabanci, ya yi godiya gare su tare da yi musu fatan alheri a gaba
  • Sababbin kwamishinonin da aka nada su ne Injiniya Mohammed Habib da Ibrahim Hala Hassan, inda suka maye gurbin wadanda aka sauke

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya yi zazzaga a gwamnatinsa domin zuba sababbin jini.

Gwamna Zulum ya sauke wasu kwamishinoni biyu daga mukamansu domin farfado da shugabanci da inganta ayyukan gwamnati.

Gwamna Zulum ya kori kwamishinoninsa 2 a Borno
Gwamna Zulum ya yi garambawul a gwamnatinsa domin inganta harkokin gwamnati. Hoto: Farfesa Babagana Umara Zulum.
Source: Facebook

Sauyin ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Dauda Iliya, ya fitar a ranar Alhamis a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana danganta matakin Zulum da ambaliyar ruwa

Kara karanta wannan

'Yadda Tinubu ya ɗauko gagarumin aiki tun na zamanin Shagari saboda ƙaunar Arewa'

Wannan matakin na zuwa ne bayan samun iftila'in ambaliyar ruwa a jiya Laraba 30 ga watan Yulin 2025.

An tabbatar da iftila'in ya jawo asarar dukiyoyi musamman yawan gidaje da suka rushe sanadin ambaliyar da aka yi.

Wasu na ganin matakin bai rasa nasaba da abin da ya faru na ambaliya musamman game da kujerar kwamishinan muhalli a jihar.

Zulum ya kori wasu kwamishinoninsa a Borno
Gwamna Babagana Zulum ya sallami wasu kwamishinoninsa. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Source: Original

Waɗanda matakin Zulum ya shafa a Borno

Wadanda abin ya shafa su ne kwamishinan muhalli, Injiniya Emat Kois, da na harkokin gwamnati na musamman, Hon. Tukur Ibrahim.

Sanarwar ta ce Gwamna Zulum ya nuna godiyarsa ga wadannan jami’ai tare da yi musu fatan alheri a ayyukansu na gaba.

Gwamnan ya bayyana cewa Injiniya Mohammed Habib da Ibrahim Hala Hassan ne za su maye gurbin wadanda aka sauke daga mukamansu.

Su wanene Zulum ya naɗa a bangaren ilimi?

Haka kuma, Gwamna Zulum ya amince da nadin Farfesa Yusuf Gana Balami a matsayin shugaban hukumar ilimin sakandare ta jihar Borno.

Balami, Farfesa a fannin ilimin kwakwalwa, ya fito daga karamar hukumar Hawul a Kudancin jihar.

Kara karanta wannan

Hotuna: An ga yadda ambaliyar ruwa ta rusa gidaje a Borno, mutane sun fara hijira

Ya yi aiki a ma’aikatar ilimi ta Borno daga 1984 zuwa 1988, sannan ya koma jami’ar Maiduguri inda ya zama farfesa a 2014.

Kwarewar da Farfesa Balami ke da shi

Farfesa Balami mamba ne a kungiyoyi masu yawa na kwararru, kuma ya rubuta littattafai da dama a matsayin jagora ko mai taimako.

Gwamna Zulum ya taya Farfesa Balami murna, ya kuma bukace shi da ya yi amfani da kwarewarsa wajen farfado da ilimin sakandare a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa dukkan nadin da aka yi an mika su ga majalisar dokoki ta jihar Borno domin tantancewa da amincewa.

Zulum ya magantu kan gaza biyan albashin N70,000

A baya, mun ku labarin cewa gwamnatin jihar Borno ta fito ta wanke kanta kan dalilin kasa biyan ma'aikatan ƙananan hukumomi mafi ƙarancin albashi.

Gwamnatin ta bayyana cewa ma'aikatan ƙananan hukumomi sun yi yawan da ba zai yiwu a riƙa biyansu mafi ƙarancin albashin ba.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya buƙaci shugabannin ƙananan hukumomi da su koma yankunansu don samun mafita kan batun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.