An Yi Rashi, Tsohon Dan Majalisa Ya Bar Duniya a dalilin Mummunan Hatsarin Mota

An Yi Rashi, Tsohon Dan Majalisa Ya Bar Duniya a dalilin Mummunan Hatsarin Mota

  • Tsohon ɗan majalisar jihar Legas, Hon. Victor Akande, ya rasu bayan haɗarin mota da ya faru a Ojo makon da ya gabata
  • Akande ya wakilci mazabar Ojo I daga 2015 zuwa 2023, ya fara ne da jam’iyyar PDP, daga bisani ya koma jam’iyyar APC
  • A majalisa, ya shugabanci kwamitin da ke kula da Shari’a, ’Yancin dan Adam, Kokensu da hukumar zabe ta Legas, LASIEC

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Jihar Legas ta yi babban rashi na tsohon dan majalisa wanda ya gamu da tsautsayin hatsari mota.

Tsohon ɗan majalisar, Hon. Victor Akande, ya rasu mako guda bayan samun hatsarin wanda ya yi sanadiyar rasa ransa.

An sanar da rasuwar tsohon dan majalisa a Legas
Tsohon dan majalisa ya rasu a Legas bayan hatsarin mota. Hoto: Lagos Gist.
Asali: Facebook

Tsohon dan majalisa ya rasu a Legas

Rahoton Tribune ya gano cewa Akande wanda ya kasance lauya ne kafin rasuwarsa ya yi bankwana da duniya ranar Laraba 30 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: An shiga jimami bayan Sarkin Gudi ya yi bankwana da duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rasu ne ranar 30 ga Yuli, sakamakon raunin da ya samu a wani haɗarin mota da ya faru a Ojo makon da ya gabata.

Akande ya yi aiki a majalisar dokoki ta jihar Legas aiki har sau biyu, inda ya wakilci mazabar jihar Legas Ojo I daga shekara ta 2015 zuwa 2023.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi alhini

Gwamnatin jihar Legas karkarshin jagorancin Gwamna Babajide Sanwo-Olu ta tura sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin a wata sanarwa a Facebook.

Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana rasuwar Hon. Akande, lauya kuma wakilin mazabar Ojo I a zaɓen majalisa na takwas da na tara, a matsayin babban rashi mai girman gaske ga kansa da mutanen Ojo da kuma jihar Legas baki ɗaya.

Gwamnan ya jajanta wa iyalan mamacin, abokansa, da sauran abokan siyasa musamman a mazabar Ojo I, inda marigayin ya wakilta tsawon shekaru takwas.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Shirin kayar da Tinubu ya kankama, an bayyana wanda zai iya gyara Najeriya a 2027

“A madadina da iyalina da gwamnatin jihar da al’ummar Legas, muna alhinin rasuwar Hon. Victor Akande.
"Labarin rasuwarsa ya girgiza ni ƙwarai, wannan babban rashi ne ga iyalinsa, jam’iyyarmu APC, da mutanen Ojo da ma jihar Lagos gaba ɗaya."
An rasa jajirtaccen tsohon dan majalisa a Legas
An shiga alhini a Legas bayan rasuwar tsohon dan majalisa. Hoto: Legit.
Asali: Original

Mukaman da marigayin ya rike a baya

An fara zaɓensa a shekarar 2015 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP kafin daga bisani ya koma jam’iyyar APC, The Nation ta tabbatar da rahoton.

Ya sake lashe zaɓe a 2019 bayan ya koma APC, ya ci gaba da zama wakili a majalisa har zuwa ƙarshen wa’adinsa a 2023.

A lokacin da yake cikin majalisa, Akande ya shugabanci kwamitin da ke kula da Hakkokin dan Adam, Kokensu, Shari’a da kuma hukumar zaɓe ta LASIEC.

Shugaban hukumar zabe a Bauchi ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa rahotanni sun tabbatar da cewa Allah ya yiwa shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi (BASIEC).

Kara karanta wannan

'Kafin 12:00 na rana': Hon. Gudaji Kazaure ya faɗi abin zai faru da Tinubu a zaɓen 2027

Marigayin Alhaji Ahmed Makama Hardawa ya rasu a Abuja a ranar Talata, 29 ga watan Yuli, 2025 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a birnin Abuja.

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi alhinin wannan rashi, inda ya miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalansa da sauran ƴan uwa da abokan arziki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.