Tinubu: Za a Fara Daukar Sunayen Manoman Gaskiya domin Raba Musu Tallafi
- Gwamnatin tarayya ta sanar da sabuwar rajistar manoma a Najeriya domin kawar da 'yan damfara a harkar noma
- Ministan harkar noma ya ce gwamnati na kokari wajen yaki da hauhawar farashi da habaka samar da abinci a Najeriya
- An ce an noma alkama fiye da kadada 133,000 yayin da ake shirin tallafa wa manoman shinkafa a Arewacin kasar nan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na tattara bayanai da kuma rajistar manoma a dukkan fadin Najeriya.
Wannan matakin na daga cikin kokarin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi domin dakile hauhawar farashin abinci a kasar nan.

Source: Getty Images
Dada Olusegun ya wallafa X cewa karamin ministan noma, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana haka a ranar Laraba a taro da aka yi a Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Abdullahi ya ce sabuwar rajistar za ta taimaka wajen kawar da ‘yan damfara da ke karbar tallafin noma ba tare da cewa suna da gonaki ba.
Amfanin daukar sunan manoma a Najeriya
Ministan noma ya ce rajistar manoman za ta bai wa gwamnati damar tantance wadanda ke aikin noma na hakika, da kuma tabbatar da cewa su kadai ke cin gajiyar tallafin gwamnati.
Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta himmatu wajen kara samar da abinci da saukaka farashi ta hanyar daukar matakai na gaggawa da kuma na dogon lokaci.
Nairametrics ta wallafa cewa ya ce umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya yi na sanya dokar ta-baci a bangaren abinci yana nan daram.
Bayanin da ya yi ya nuna cewa gwamnati ta riga ta noma alkama kadada 133,000 a jihohin Arewa 15, kuma jihar Jigawa ta taka rawa sosai inda aka noma sama da kadada 50,000.
Shiri ga manoman shinkafa a Najeriya
Ministan ya ce gwamnati na shirin tallafa wa manoman shinkafa har 44,500 tare da ba su horo da kuma samar da manyan injina na zamani da za su taimaka wajen kara yawan amfanin gona.
Sanata Abdullahi ya bayyana cewa an kawo motacin noma kirar tractor 2,000 daga kasar Belarus da kuma kayayyakin aikin noma 9,000 domin tallafa wa manoma a fadin kasar.
Ya ce ana cigaba da bunkasa yankunan sarrafa amfanin gona (SAPZs) domin saukaka kasuwanci da taimaka wa manoma su rika samun riba mai yawa daga kayan da suka noma.

Source: Twitter
Samar da iri da dam don habaka noma
A bangaren bincike, ministan ya bayyana cewa cibiyoyin bincike sun fitar da sababbin nau’in kayan gona, ciki har da irin tumatur da ya fi karfin cutar da ake kira “tomato Ebola”.
Ya ce a bangaren kiwo kuma, gwamnati na gina rugage, kauyukan kiwo da matsuguni na dabbobi, tare da kaddamar da wata sabuwar manhaja ta kiwon shanu da shanun madara.
A karshe, ministan ya bukaci shugabannin Arewa da su hada kai wajen kawar da masu amfani da bayanan bogi domin karbar tallafi a madadin manoma na gaskiya.
NNPCL zai cigaba da tono mai a Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin man Najeriya na NNPCL ya bayyana kokarin da Bola Tinubu ya ke wajen cigaba da hako mai a Arewa.
NNPCL ya ce ya yi nasarar tono rijiyoyin man fetur hudu a Kolmani da aka fara hako mai tun zamanin shugaba Muhammadu Buhari.
Baya ga haka, NNPCL ya ce yana shirin kafa wasu cibiyoyin iskar gas a jihar Kogi da za su saukaka rayuwar al'ummar Arewa da Najeriya baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


