'Za a Rataye Shi': Kotu Ta Yanke wa Malamin Musulunci Hukuncin Kisa a Jihar Kwara

'Za a Rataye Shi': Kotu Ta Yanke wa Malamin Musulunci Hukuncin Kisa a Jihar Kwara

  • Kotu ta yanke wa Malam Abdulrahman Bello hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe dalibar kwaleji
  • Amma Mai shari’a Hannah Ajayi ta wanke mutum hudu da ake zargi da hannu a kisan Hafsoh Lawal, saboda rashin shaidu da hujjoji
  • Rahotanni sun nuna cewa Malam Abdulrahman ya kashe Hafsoh ne domin tsafi da nufin samun kudi da kuma safarar sassan jikinta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Wata babbar kotun jihar Kwara da ke da zama a Ilorin, babban birnin jihar ta yankewa malamin Musulunci, Abdulrahman Bello hukuncin kisa.

Kotun ta ce za a rataye Abdulrahman Bello har lahira bayan da aka same shi da laifin kashe Hafsoh Lawal, dalibar ajin karshe a kwalejin ilimi ta Ilorin.

Kotu a Kwara ta kama Malam Abdulrahman da laifin kisan kai, ta yanke masa hukuncin rataya
Za a rataye Malam Abdulrahman Bello bayan samunsa da laifin kashe Hafsoh Lawal a Kwara. Hoto: @Justolaola, @insideilorin
Source: Twitter

Kotu ta wanke mutum 4 daga zargin kisa

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya fara gwangwaje jihohin Arewa da titunan jiragen kasa

Channels TV ta rahoto cewa Mai shari'a Hanna Ajayi, ta babbar kotun jihar ce ta yanke wannan hukunci a ranar Alhamis.

Mai shari'a Hannah Ajayi ta kuma wanke wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a kisan tare da sakinsu, bayan gaza samunsu da wani laifi.

Da farko, kotun ta fara wanke hudu daga cikin mutane biyar da ake zargi daga laifin kashe dalibar, bayan an tuhume su da laifuffuka biyar.

Wadanda aka wanke sun hada da Ahmed Abdulwasiu, Jamiu Uthman, Suleiman Muyideen da kuma Abdulrahman Jamiu.

Kotun ta ce ba ta samu wadannan mutane hudu da hannu a kisan Hafsoh Lawal ba, don haka ta wanke su daga dukkanin tuhume-tuhumen biyar.

Kwara: An yankewa malami hukuncin kisa

Yayin da take yanke hukunci a kan babban mai laifin, Abdulrahman Bello, Mai Shari’a Hannah Ajayi ta bayyana kisan Hafsoh a matsayin zalunci, mugunta, da kuma tsantsar rashin imani na dan Adam.

BBC ta rahoto alkaliyar ta ce duk wasu hujjoji sun tabbatar da cewa an kashe Hafsoh ne kawai don a yi tsafi da nufin samun kudi da kuma safarar sassan jikinta.

Kara karanta wannan

Katsina: Kotu ta yanke hukuncin kisa ga mutum 2 kan kisan tsohon kwamishina

Mai shari'ar ta ce ikirarin da Malam Abdulrahman ya yi na cewar yana son Hafsoh, kuma har yana shirin aurenta, karya ce tsagwaronta, kuma ya yi hakan ne don ya jawo ta zuwa gidansa inda ya kashe ta.

Don haka ne ta yanke wa Abdulrahman Bello hukuncin kisa ta hanyar rataya, yayin da ta saki sauran mutane hudu da ake zargi, bayan gaza samunsu da laifi.

Rahotanni sun ce Malam Abdulrahman ya kashe Hafsoh Lawal don tsafi da ita da sayar da sassan jikinta
Kotun Ilorin ta yanke wa Malam Abdulrahman Belo hukuncin kisa ta hanyar rataya kan kashe Hafsoh Bala. Hoto: @justeventsonlin
Source: Twitter

Yadda malamin ya kashe Hafsoh Lawal

An rahoto cewa an aikata laifin ne a ranar 10 ga Fabrairun 2025 a yankin Olunlade da ke Ilorin watau babban birnin jihar Kwara.

An ce Abdulrahman ya gayyaci Hafsoh, wanda saurayinta ne zuwa gidansa, inda ya kashe ta, ya kuma daddatsa sassan jikinta a dakinsa, bayan ya gama lalata da ita.

Bayan an cafke shi kuma an tuhume shi, an samu sassan jikin mamaciyar da jini cike da kwalba, da kuma kayayyakinta a dakin Abdulrahman.

An kuma samu addar da ake kyautata zaton da ita ce malamin ya yi amfani da ita wajen aikata wannan danyen aikin.

Daga bisani ne kuma aka gano wasu sassan jikin nata da suka fara rubewa a wani juji da ke Ilorin.

Kara karanta wannan

Siyasa: Rikici ya yi kamari a SDP, an tura mutanen El Rufa'i kurkuku

An kai Malam Abdulrahman gidan yari

Tun da fari, mun ruwaito cewa, kotu ta ba da umarnin a tsare malamin Musulunci, Abdulrahmam Mohammed, kan zargin kisan Hafsoh Bala.

Ana zargin malamin tare da wasu mutum huɗu da haɗa baki wajen kashe ɗalibar ajin karshe a kwalejin ilimi ta jihar Kwara, don neman kudi ta hanyar tsafi.

Ana tuhumar Abdulrahman da mutane hudu da laifuffukan da suka haɗa da haɗa baki wajen aikata laifi, kisan kai, fashi da makami da mallakar sassan jikin ɗan adam.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com