Shugaba Tinubu Ya Cika Alkawarin Samar da Tsaro a Najeriya, An Kafa Hujja da Jihohi 2

Shugaba Tinubu Ya Cika Alkawarin Samar da Tsaro a Najeriya, An Kafa Hujja da Jihohi 2

  • Samar da tsaro a Arewa da sauran sassan Najeriya na ɗaya daga cikin muhimman alkawurran da Bola Tinubu ya ɗauka kafin zaɓe
  • Shekaru biyu bayan hawa mulki, fadar shugaban ƙasa ta fara ikirarin cewa Tinubu ya samar da tsaro a Najeriya
  • Hadimin shugaban ƙasa, Daniel Bwala ya bayar da hujjojin da yake ganin cewa tsaro ya samu a Kudu da Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta bayyana yadda Bola Ahmed Tinubu ya cika alkawarin da ya ɗaukar wa ƴan Najeriya game da tsaro.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan sadarwa, Daniel Bwala, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta cika alkawarin ta ga ‘yan Najeriya wajen samar da tsaro a ƙasar.

Hadimin shugaban ƙasa, Daniel Bwala.
Fadar shugaban ƙasa ta yi ikirarin cewa Shugaba Tinubu ya cika alkawari kan tsaro Hoto: @BwalaDaniel
Source: Twitter

Bwala ya bayyana haka ne a wani shirin siyasa na kafar watsa labarai ta Channels TV a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

ADC: 'Yadda gwamnoni da hadimai ke cika kunnen Tinubu da karya da gaskiya'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin ya ba da misali da Benuwai da Filato

“Ya yi alkawurra kan wutar lantarki, amma mu ɗauki abubuwa masu muhimmanci, alkawari na farko, tsaron rayuka da walwalar al’umma su ne nauyin gwamnati.
"Ka duba yanzu shiri mu ke gudanarwa a nan, amma a da, ka san yadda kake yawo a cikin ƙasar nan. Bari in tambaye ka, da ma ‘yan Najeriya gaba ɗaya. Kwanan nan, mun fuskanci matsalolin tsaro masu muni a Benuwai, ba su ragu ba? Muna da matsala a Filato. Ba ta ragu ba?
"Ka duba batun IPOB, da kuma ‘yan bindiga. Ka san yadda kisan kai ya yawaita a can a 2022, 2023. Ka san yadda sace mutane daga gidajensu a tsakiyar gari ya zama ruwan dare a baya.”

- Daniel Bwala.

Bwala ya ce Tinubu ya samar da tsaro

Bwala ya ƙara da cewa an rage matsalar rashin tsaro matuƙa, inda ya kara da cewa ɗaiɗaikun hare-haren da ake kai wa yanzu ba su da alaƙa da gazawar gwamnati don suna faruwa a ko'ina a duniya.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Dakarun Sojoji sun hallaka ƴan bindiga sama da 3,000 a jihohin Arewa

“Matsalar rashin tsaro ta ragu sosai. Abin da muke gani a Najeriya yanzu, laifuffukan ɗaiɗaiku ne waɗanda ba su da alaƙa da gazawar shugaba, domin suna faruwa a ko’ina a duniya.”
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Fadar shugaban ƙasa ta ce tattalin arziki ya farfaɗo a mulkin Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Wane hali tattalin arzikin Najeriya ke ciki?

Game da halin da tattalin arzikin ƙasa ke ciki, Bwala ya ce Najeriya tana kan hanyar murmurewa gaba ɗaya.

Ya ƙara da cewa samun ƙarin kuɗaɗen shiga a ƙasar ya sa gwamnoni ke jin daɗin wani yanayi kamar “lokacin arzikin man fetur” a ƙarƙashin mulkin Tinubu.

Bisa haka, Bwala ya yi fatali da haɗakar ƴan adawa, yana mai cewa ba wata barazana ba ce ga kudirin tazarcen Shugaba Tinubu, Vanguard ta rahoto.

Sojoji sun murƙushe ƴan bindiga 3000

A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun sheƙe ƴan bindiga sama da 3,000 cikin shekarƴ biyu a Arewacin Najeriya.

Babban hafsan tsaro na ƙasa, Jamar Christopher Musa ya ce sojojin Najeriya aun samu nasarori da dama a fannin tsaro daga rantsar da Tinubu zuwa yau.

Bugu da ƙari ya ce sojoji sun karɓi miyagu aƙalla 120,000 waɗanda suka miƙa wuya a sassa daban-daban na kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262