Bola Tinubu Ya Fara Gwangwaje Jihohin Arewa da Titunan Jiragen Kasa

Bola Tinubu Ya Fara Gwangwaje Jihohin Arewa da Titunan Jiragen Kasa

  • Ministan sufuri na kasa ya ce an fara aikin layin dogo a Kaduna da Kano don inganta sufuri da tattalin arziki
  • Gwamnatin tarayya ta kammala gidaje 3,112 a Abuja da wasu 1,000 a jihar Kano da sauran jihohi shida na Arewa
  • Rahoto ya nuna cewa ayyukan za su samar da ayyukan yi fiye da 250,000 tare da jawo zuba jari na biliyoyin Naira

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin inganta sufuri ta hanyar aikin layin dogo a wasu jihohin Arewa, inda Kaduna da Kano suka fara cin gajiyar shirin.

Wannan wani bangare ne na kokarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen bunkasa rayuwar jama'a da saukaka zirga-zirga.

An fara kafa jiragen kasa a jihohin Arewa
Gwamnatin Tinubu ta ce an fara kafa jiragen kasa a jihohin Arewa. Hoto: Bayo Onanuga|NRC
Source: Twitter

Legit ta tattaro bayanan ne a cikin wani sako da ma'aikatar yada labarai da wayar da kan al'umma ta wallafa a X.

Kara karanta wannan

Hako fetur a Arewa: Kamfanin NNPCL ya tono rijiyoyin mai 4 a Kolmani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan sufuri, Sanata Sa’idu Ahmed Alkali, ne ya bayyana haka yayin wani taron tattaunawa a jihar Kaduna wanda gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta shirya na tsawon kwana biyu.

Ana samar da jirgin kasa a yankin Arewa

Ministan ya bayyana cewa an fara aikin layin dogo a Kaduna da Kano domin kara saukin sufuri da karfafa harkokin kasuwanci a yankin.

Ya kara da cewa shirin zai kasance babbar hanyar bunkasa biranen Arewa da rage dogaro da motocin haya, musamman ga masu karamin karfi.

A cewar ministan, ayyukan za su kasance da hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu don tabbatar da inganci da dorewa kuma daga baya za a tsunduma sauran jihohi.

Gwamnatin Tinubu ta gina gidaje a Arewa

Dangane da shirin Renewed Hope Cities (RHC), Alkali ya bayyana cewa an kammala gine-ginen gidaje 3,112 a Abuja.

Ministan ya kara da cewa Kano ta samu gidaje 1,500, sai wasu karin gidaje 500 a wani sabon rukunin gini da ke kan hanya.

Kara karanta wannan

2027: Manyan Arewa sun rabu 2, wasu na sukar Tinubu wasu na goyon baya

The Cable ta rahoto ya ce a wasu jihohin Arewa da suka hada da Sokoto, Gombe, Yobe, Katsina, Nasarawa da Benue, an kammala gina gidaje 250.

Matasa za su samu aikin ₦150,000 a wata

Ministan ya bayyana cewa aikin zai samar da fiye da ayyukan yi 250,000 a wuraren aikin da dama a fadin kasar.

A cewar shi, ma'aikata za su samu albashi da ya kai ₦150,000 a kowane wata, wanda zai inganta rayuwarsu da ta iyalansu.

Baya ga haka, Sai'idu Alkali ya ce shirin zai jawo masu zuba jari da za su zuba kudin da zai kai darajar ₦70bn.

Ministan sufurin Najeriya yayin ziyarar duba aiki
Ministan sufurin Najeriya yayin ziyarar duba aiki. Hoto: Sa'idu Ahmed Alkali
Source: Twitter

Haka kuma, za a bude cibiyoyin kayan gini a wuraren da ake aikin, wanda zai kara bunkasa tattalin arziki.

Ministan ya ce aikin sabunta layin dogo na zamani daga Kaduna zuwa Kano ya kai kashi 53, haka kuma, aikin daga Kano zuwa Maradi ya kai kashi 61 cikin 100.

Manyan Arewa sun rabu 2 kan Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa an samu rabuwar kai tsakanin manyan Arewa game da salon mulkin Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

2027: Ana lallaba Atiku da sauran 'yan Arewa su hakura sai Tinubu ya yi tazarce

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na cikin manyan Arewa da suka koka da cewa gwamnatin Tinubu ta yi watsi da Arewa.

Sai dai a daya bangaren, shugaban gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce Tinubu ya cika alkawuran da ya yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng