Amnesty Int'l ta yi Allah Wadai da DSS bayan Cafke Matashi kan Ƴada 'Mutuwar' Tinubu

Amnesty Int'l ta yi Allah Wadai da DSS bayan Cafke Matashi kan Ƴada 'Mutuwar' Tinubu

  • Amnesty International ta zargi DSS da cin zarafin ɗan adam saboda kama da tsare Ghali Isma’il wanda aka fi sani da Sultan
  • Ana zargin jami'an DSS da cafke matashin saboda wani bidiyo da ake ce ya haɗa a kan rashin lafiyar shugaban ƙasa
  • Shugaban Amnesty Int'l dake fafutukar kare hakkin ɗan adam a Najeriya, Isa Sanusi ya ce DSS ta gaza nuna ƙwarewa a kan batun

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya, Amnesty In'l, ta soki ci gaba da tsare shahararren mai amfani da Tiktok, Ghali Isma’il.

Jami'an tsaron farin kaya (DSS) ne suka damƙe matashin da aka fi sani da Sultan a kan bidiyon da ya shafi lafiyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Abin da DSS suka yi wa ɗan TikTok da ake zargin ya ce Tinubu ya mutu sanadin guba

DSS da ɗan Tiktok Ghali Isma'il
Amnesty Int'l ta caccaki DSS Kan kama dan Tiktok Hoto: Hamza Nuhu Dantani
Asali: Facebook

A gargaɗin da Amnesty Int'l ta wallafa a Facebook, ta bayyana kama da tsare Sultan da cewa alama ce take hana faɗin albarkacin baka a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amnesty Int'l ta caccaki DSS, Tinubu

Amnesty ta bayyana kama wa da tsare Ghali da hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta yi matsayin babban misalin cin zali da keta mutuncin ɗan adam.

A zantawa da Legit, shugaban ƙungiyar na Najeriya, Isa Sanusi ya ce:

"Muna Allah wadai da babbar murya a kan kama Ghali Isma'il da aka yi."
"Mu a ganinmu cewa ana nema ne a gallaza masa, a ci mutuncinsa, domin ƴan Najeriya kowa na da yanci ya faɗi ra'ayinsa."

Sanusi ya ce duk da ba su goyon bayan jama'a su riƙa yaɗa ƙarya ko faɗin maganguna da za su yamutsa hazo, amma Ghali bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba.

Ya ce wannan na nuna gazawar gwamnatin Bola Tinubu wajen ɗaukar suka ko wasu kalamai da ba su yi mata daɗi ba.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya yi fatali da tsarin jam'iyya mai mulki, ya yi barazanar sauya sheƙa

Amnesty ta yi bincike kan Ghali Ismail

Ƙungiyar Amnesty ta bayyana mamakin yadda gwamnati da jami'an DSS suka gaza gudanar da cikakken bincike a kan matashin da aka kama.

A kalaman shugaban ƙungiyar:

"Mun yi bincike mun gano cewa wannan bidiyo sharri aka yi masa aka sa hotonsa, ba shi ya yi ba."
"Ko da shi ne ya yi, bai kamata a ce saboda wannan a kai shi kotu ba, ko a ɗaure shi ba, domin kowace ƙasa, a tsari da muke da shi, kowa na da ƴancin ya faɗi albarkacin bakinsa."

Amnesty Int'l ta kara da cewa wasu ne suka haɗa hoton Tinubu da fasahar AI, sannan aka ɗauko bidiyon Ghali aka ɗora a kai.

Ta buƙaci jami'an DSS da su riƙa nuna ƙwarewa a aiki, tare da neman a saki Ghali nan take ba tare da sharadi ba.

Jami'an DSS sun dura kan ɗan Tiktok

Kara karanta wannan

Dattawa sun faɗi dalilan da suka jawo Arewa ta tsaya cak, babu cigaba a Najeriya

A baya, mun wallafa cewa wani lauya kuma mai kare haƙƙin bil’adama, Barrister Hamza Nuhu Dantani, ya caccaki hukumar DSS Kan zargin take hakkin Ghali Isma'il.

Hamza Nuhu Ɗantani ya bayyana cewa jami’an DSS sun tilasta wa Sultan ya bayar da bayanan sirrin wayarsa bayan an zarge shi da yaɗa 'mutuwar' Bola Tinubu.

Har yanzu dai DSS ba ta bayyana binciken da aka gudanar a kan matashin ba, yayin da ƙungiyoyi da dama ke ci gaba da neman a saki Ghali Isma'il.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.