Nasara daga Allah: Dakarun Sojoji Sun Hallaka Ƴan Bindiga Sama da 3,000 a Jihohin Arewa

Nasara daga Allah: Dakarun Sojoji Sun Hallaka Ƴan Bindiga Sama da 3,000 a Jihohin Arewa

  • Gwamnatin Tarayya na ci gaba da bayyana ci gaban da ta samu a ɓangarori daban-daban bayan rantsar da Bola Tinubu a watan Mayu, 2023
  • Babban hafsan tsaro na ƙasa, Jamar Christopher Musa ya ce sojojin Najeriya aun samu nasarori da dama a fannin tsaro
  • Daga cikin waɗannan nasarori, Janar Musa ya ce sojoji sun aika dubban ƴan ta'adda lahira a Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babban Hafsan Tsaro na Ƙasa (CDS), Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa dakarun sojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga sama da 3,000 cikin shekaru biyu a Arewa.

Musa ya ce sun kuma karbi miyagu akalla 120,000 da suka miƙa wuya tare da ceto mutane fiye da 2,000 da aka sace a jihohin Arewacin Najeriya cikin shekaru biyu da suka gabata.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP, an tura miyagu barzahu

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa.
Sojoji sun tura ƴan ta'adda 3,000 lahira a shekara 2 Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na hedkwatsar tsaron Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar a ranar Laraba, Tribune Nigeria ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Janar Musa ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin gabatar da jawabi a taron tattaunawa tsakanin gwamnati da jama'a, wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna.

Yadda sojoji suka kashe ƴan bindiga 3,000

Hafsan tsaro ya ce:

“A cikin shekaru biyu da suka gabata, mun kashe sama da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga 3,000, mun ceto fiye da mutane 2,000 da aka yi garkuwa da su.
"Haka nan mun kwato makamai sama da 2,300 da harsashi 72,000 a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya da muka kafa rundunar sojoji.

Bugu da ƙari, Christopher Musa ya ce dakarun tsaro sun karɓi ƴan ta'adda sama da 120,000 da suka miƙa wuya a tsawon shekarun da ake magana a kai.

Kara karanta wannan

'Ban da Peter Obi': An yi wa Malami wahayi game da mutum 3 da za su fatata a 2027

Ci gaban da Janar Musa ya kawo a Najeriya

Ya kuma jaddada wasu muhimman nasarori da aka samu tun bayan hawansa shugabancin sojin Najeriya, ciki har da kafa Cibiyar Horo da Tsare-Tsaren Yaƙi ta Sojoji a Abuja.

A cewar sanarwar, rundunar sojin Najeriya ta yaye ƙwararrun jami'ai 800 da suka kammala horo, yayin da ɗaruruwan wasu ke cigaba da karɓar horo a Jaji da jihar Nasarawa domin ƙara gogewa a yaƙi da ta’addanci da garkuwa da mutane.

Dakarun sojojin Najeriya.
Janar Musa ya ce an samu ci gaba a rundunar soji bayan ya karɓi aiki Hoto: @DHQNigeria
Source: Facebook

Janar Musa ya ƙara da bayyana cewa a cikin sababbin matakan ƙarfafa ayyukan sojoji, an sake fasalta rundunar da ke aiki a yankin Arewa maso Yamma zuwa Operation Fansan Yamma.

Ya ce an ƙirƙiri sababbin ruundunoni na musamman a jihohin Kaduna da Neja, domin faɗaɗa ayyukan sojida girke dakarun da za su kare rayuwa da dukiyoyin al'umma, rahoton Bussiness Day.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun rundunar sojin Najeriya sun daƙile harin ƴan ta'addan Boko Haram a Monguno da Bitta da ke jihar Borno.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan barkewar rikicin kabilanci a Abuja, an tafka barna

A yayin artabun da suka yi, dakarun sojojin sun samu nasarar kashe mayaka da dama ciki har da wani babban kwamandan Boko Haram.

Bayan haka sojojin sun kwato makamai da alburusai daga hannun ƴan ta'addan, kana suka bi sawun waɗanda suka tsere.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262