An Zo Wajen: Kamfanin NNPCL Ya Yi Magana kan Sayar da Matatar Port Harcourt
- Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya kawo karshen jita-jita dangane da batun sayar da matatar mai ta Port Harcourt da ke jihar Rivers
- Shugaban kamfanin NNPCL, Bashir Bayo Ojulari, ya ce babu shirin sayar da matatar wacce aka dakatar da aiki da ita a kwanakin baya
- Ya nuna tun da farko an yi kuskure wajen fara da amfani da matatar kafin a kammala gyaranta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya yi magana kan sayar da matatar mai ta Port Harcourt.
Kamfanin na NNPCL ya bayyana a hukumance cewa ba zai sayar da matatar mai ta Port Harcourt ba, yana mai jaddada aniyarsa ta kammala gyaranta da kuma ci gaba da riƙe matatar.

Asali: Twitter
Jaridar The Punch ta ce shugaban kamfanin NNPCL, Bashir Ojulari, ne ya bayyana hakan a yayin taron tattaunawa da ma’aikata da aka gudanar a ranar Talata, 28 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dai gudanar da taron ne a hedkwatar kamfanin NNPCL dake birnin tarayya Abuja, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
NNPCL ba zai saida matatar Port Harcourt ba
Ya bayyana cewa wannan matsayar ba sauyin ra’ayi bane, sai dai an cimma ta ne sakamakon cikakkiyar bitar da ake gudanarwa a kan matatun mai na Port Harcourt, Kaduna da Warri.
“Ina mai bayyana cewa nazarin da ake yi yanzu ya nuna cewa matakin da aka ɗauka a da na fara aiki da matatar Port Harcourt kafin a kammala cikakken gyaranta ya kasance mara kyau kuma ba ya da alfanu a kasuwanci."
- Bashir Bayo Ojulari
Duk da cewa ana samun ci gaba a kan dukkanin matatun guda uku, ya bayyana cewa bayanan da ke fitowa yanzu sun nuna cewa akwai buƙatar haɗin gwiwa da ƙwararrun abokan hulɗa a fannin fasaha domin kammala aikin gyara da kuma haɓaka ingancin matatun.
Jawabin Ojulari ya samu maraba da tafi daga ɗaruruwan ma’aikatan da suka halarci taron, waɗanda suka nuna jin daɗinsu da mayar da hankali kan dabarar kasuwanci da kuma riƙe kadarorin kamfani.
Matsayar shugaban na NNPCL ta yi daidai da manufofin gwamnatin tarayya kan samar da tsaron makamashi, inda take ci gaba da nuna aniyarta na riƙe muhimman kadarorin makamashi a hannun gwamnati a yayin da ake ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a sashen makamashi.

Asali: Twitter
Karanta wasu labaran kan kamfanin NNPCL
- Shugaban NNPCL ya samu matsala da majalisa kan ɓacewar N210trn
- Sauki ya samu: 'Yan kasuwa sun dawo da farashin fetur kasa da na Dangote, NNPCL
- EFCC ta fadi sunayen jami'an NNPCL da suka 'sace' kudin matatun mai bayan kama su
Kamfanin NNPCL ya rage farashin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya rage farashin fetur a gidajen man da suke mallakinsa.
Kamfanin NNPCL ya rage farashin da ake siyar da fetur a birnin tarayya Abuja zuwa N890 a kan kowace lita.
Rage farashin dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gasa tsakanin kamfanin NNPCL da matatai mai ta Dangote.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng