Gwamnatin Tinubu Za Ta Samar da Ayyuka a Kaduna, Za a Farfado da Masaka

Gwamnatin Tinubu Za Ta Samar da Ayyuka a Kaduna, Za a Farfado da Masaka

  • Gwamnatin tarayya za ta farfado da kamfanin auduga na Kaduna domin bunkasa masana’antu da tattalin arzikin Najeriya
  • Sanata George Akume ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu na aiki tukuru a fannoni takwas don ganin an samu ci gaba a ƙasar
  • A baya dai hukumar haraji ta Kaduna ta rufe kamfanin sarrafa auduga na UNTL saboda bashin haraji da ya kai Naira biliyan 1.2

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Gwamnatin tarayya ta ce za ta farfado da kamfanin sarrafa auduga na Kaduna da tuni ya durkushe, domin inganta tattalin arzikin ƙasar.

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya bayyana hakan a taron tattaunawa kan nasarorin mulkin Shugaba Bola Tinubu a Kaduna.

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta farfado da kamfanin auduga na Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Hoto: @ubasanius
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta rahoto cewa kungiyar tunawa da marigayi Sir Ahmadu Bello ce ta shirya taron mai taken: "Nazarin alkawuran zaɓe: Ƙarfafa dangantakar gwamnati da jama’a domin haɗin kan kasa."

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan barkewar rikicin kabilanci a Abuja, an tafka barna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati za ta farfado da kamfanin auduga

An ruwaito cewa Akume ne ke jagorantar tawagar gwamnatin tarayya, wadda ta ƙunshi dukkanin waɗanda Tinubu ya ba mukami a Arewacin ƙasar.

A cewar Sanata Akume, burin Shugaba Tinubu shi ne ya ga an inganta kowane yanki a Najeriya, kuma ya ci alwashin cimma hakan.

"Tinubu yana aiki tukuru a manyan fannoni guda takwas domin tabbatar da cigaba mai ɗorewa a faɗin ƙasar.
"Gwamnatin Tinubu na da shirin bunƙasa masana’antu domin rarraba hanyoyin samun kudaden shiga. Muna da shirin farfafo da kamfanin auduga na Kaduna da sauran manyan masana’antun Arewa.
"Za mu dawo da waɗancan kyawawan lokutan da kamfanin sarrafa auduga na Kaduna yake matsayin wata babbar masana'antar bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
"Za a aiwatar da wannan da wasu muhimman abubuwa a gwamnatin Tinubu, wadda bayan shekara biyu da wata biyu a ofis, ta riga ta cimma wasu ayyukan da dama"

Kara karanta wannan

Uba Sani ya faɗi abin da Tinubu yake yi da ba a taɓa shugaban ƙasa da ya yi ba

- Sanata George Akume.

Manyan jami'an gwamnati sun halarci taron

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rahoton cewa waɗanda suka halarci taron sun haɗa da ministan yaɗa labarai da tsare-tsaren kasa, Alhaji Mohammed Idris.

Sauran sun hada da ministan harkokin mata, Hajiya Imaam Suleiman-Ibrahim, da shugaban ma’aikatar tsaro ta kasa, Janar Christopher Musa.

Hakazalika, akwai shugaban hukumar NAN, Malam Ali M. Ali, da shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) da sauransu.

Sanata George Akume ya ce shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin farfado da masana'antun Arewa
Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya fadi shirye-shiryen Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @SGFAkume
Source: Twitter

KADIRS ta rufe kamfanin auduga na Kaduna

Tun da fari, an ruwaito cewa hukumar haraji ta Kaduna (KADIRS) ta rufe kamfanin auduga na Kaduna saboda bashin haraji da ya kai Naira biliyan 1.2.

Kamfanin UNTL shi ne kamfanin sarrafa auduga na ƙarshe da ya rage yana aiki a Kaduna, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A baya, kamfanin UNTL wanda shi ne mafi girma a yammacin Afirka, ya kasance yana da ma’aikata kusan 10,000 kafin ya dakatar da samar da kaya a shekarar 2007.

Kara karanta wannan

2027: Ana lallaba Atiku da sauran 'yan Arewa su hakura sai Tinubu ya yi tazarce

Bayan rufe kamfanin, Barista Aysha Ahmad, sakatariya kuma mashawarciyar shari’a ta KADIRS, ta ce bashin harajin ya haɗa da na haya, sabis na kashe gobara, KEPA da sauran haraji da ake bin kamfanin a jihar.

'An yi watsi da Arewa' - Kwankwaso ga Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Rabiu Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan abin da ya kira watsi da Arewacin Najeriya.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya zargi gwamnatin APC mai ci da karkatar da hankalinta wajen gina yankin Kudu da albarkatun ƙasar nan.

Sanata Kwankwaso ya ce titunan Arewa sun lalace matuƙa, inda ya shawarci shugaban ƙasa ya yi adalci wajen raba albarkatu tsakanin Arewa da Kudu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com