Gwamnati za Ta Fuskanci Kalubale, An Maka Tinubu a gaban Kotun Tarayya

Gwamnati za Ta Fuskanci Kalubale, An Maka Tinubu a gaban Kotun Tarayya

  • Wani mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Dr Bolaji Akinyemi, ya shigar da kara a kotu yana kalubalantar shugaban Najeriya, Bola Tinubu
  • Dr. Akinyemi ya shigar da karar ne yana kalubalantar sahihancin tsawaita wa’adin shugaban kwastam, Bashir Adeniyi da wa'adinsa ya kare
  • Mai karar na neman kotu ta hana ci gaba da wa’adin Adeniyi da kuma yanke hukunci cewa hakan ya saba wa kundin tsarin mulki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Wani mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Dr Bolaji Akinyemi, ya shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas kan tsawaita wa'adin shugaban kwastam.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya yi fatali da tsarin jam'iyya mai mulki, ya yi barazanar sauya sheƙa

Dr. Akinyemi na kalubalantar sahihancin ko rashin sahihancin tsawaita wa’adin Shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

Shugaban kasa, Bola Tinubu
Mai fafutuka ya maka shugaban kasa a gaban kotu Hto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a cikin karar mai lamba (FHC/L/CS/1495/2025), an ambaci Shugaba Bola Tinubu; Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, a matsayin wadanda ake kara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da Ministan Kudi, Wale Edun; Hukumar Kwastam ta Najeriya; Hukumar Gudanarwar Kwastam; Ofishin Shugaban Kwastam da Haraji na Najeriya; da kuma shugaban Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi.

Dalilin kai Bola Tinubu gaban kotu

Jaridar Independent ta bayyana cewa Lauyan wanda ya shigar da karar, Newworth LLP, ya ce karar ta kalubalanci tsawaita wa’adin Mista Adeniyi a gaban ofis bayan kammala wa'adinsa a 5 ga Mayu, 2025.

A cewar lauyan mai karar, batutuwan da kotu su ke bukatar kotu ta yanke hukunci a kai sun hada da:

“Ko shugaban kasa na da hurumin kundin tsarin mulki ko doka a karkashin sashi na 14(1) na dokar Hukumar Kwastam ta 2023 (da aka sabunta) da ke ba shi damar tsawaita wa’adin Mista Adeniyi."

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa ta kalubalanci masu sukar $100,000 da gidajen da Tinubu ya ba Falcons

“Ko Mista Adeniyi na da hurumin ci gaba da aiki a matsayin shugaban kwastam bayan karewar wa’adinsa ba tare da keta ‘yancin jama’a da tsarin mulki ba.”

Bukatar Akinyemi a kotun tarayya

Mai karar na neman kotu ta yanke hukunci da ke bayyana duk wani yunkurin tsawaita wa’adin Mista Adeniyi a matsayin abin da ya saba doka ba kuma sabawa kundin tsarin mulki.

Ya kuma bukaci a ba da umarnin hana shugaban kasa da Mista Adeniyi aiwatar da ko karɓar duk wani sabon wa’adi na cigaba da aiki.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Ana zargin gwamnatin Tinubu da kara wa'adin shugaban Kwastam Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Haka kuma mai karar ya bayyana cewa duk wani karin umarni da kotu za ta ga ya dace domin kare tsarin mulki da bin doka a kan batun ya yi daidai.

'Yan gwagwarmaya sun shigar da Tinubu kotu

A wani labarin, mun wallafa cewa saboda matsalolin tsaro da rikicin siyasa a Zamfara, wasu lauyoyi masu fafutukar kare hakkin jama'a sun shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Lauyoyin, Reuben Boma, Okoro Nwadiegwu, da kuma ƙungiyar One Love Foundation ne suka shigar da ƙarar, suna son a tilasta wa Bola Tinubu ayyana dokar ta baci a jihar.

Sun roƙi kotu ta umurci Shugaban Ƙasa ya ayyana dokar ta-baci domin kawo karshen rikice-rikicen da ke hana zaman lafiya da cigaba a jihar Zamfara, kamar yadda aka yi a Ribas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng