Mabambantan Ra’ayoyi daga Malaman Musulunci game da Yafewa Marigayi Buhari
An sanar da rasuwar marigayi Muhammadu Buhari a yammacin ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2025 da muke ciki bayan fama da jinya.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Marigayi tsohon shugaban kasa ya rasu ne bayan fama da doguwar jinya a birnin London da ke kasar Birtaniya.

Source: Twitter
Umarnin da Tinubu ya bada bayan rasuwar Buhari
Rasuwarsa ke da wuya Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa, Kashim Shettima ya je ya taho da gawarsa zuwa Najeriya kamar yadda hadiminsa, Bayo Onanuga ya sanar a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shettima ya isa London inda ya jajantawa iyalan marigayi tare da dawo da shi Najeriya domin yi masa sallar jana'aza, Punch ta ruwaito.
Daga karshe, an gudanar da sallar jana'izar marigayin a ranar Talata 15 ga watan Yulin 2025 a garin Daura da ke jihar Katsina.
Hayaniya da ta biyo bayan rasuwar Buhari
Sai dai abin da ya fi daukar hankali bayan rasuwar Buhari shi ne ce-ce-ku-ce da ake ta yi na cewa wasu ba su yafe masa ba.
An samu rarrabuwar kawuna yayin da wasu tun ranar da ya rasu suka ce sun yafe hakkinsu kuma suka yi masa addu'ar samun rahama.
Lamarin bai tsaya iya kan talakawa ba hatta malaman Musulunci a Arewacin Najeriya sun tattauna kan lamarin.
Legit Hausa ta duba ra'ayoyin malaman Musulunci kan maganar yafewa Buhari ko sabanin haka.
1. Sheikh Lawan Abubakar Triumph
Kusan Sheikh Triumph shi ya fara magana kan wannan lamari bayan rasuwar marigayi Muhammadu Buhari da Tijjanee Muhammad ya wallafa a Facebook.
Shehin ya ce gwara Buhari an ga ƙarshensa ya mutu cikin iyalansa an dauko shi an yi masa sallar kai ka san ya kaeshenka zai kasance.
Ya ce matar Buhari ta nema masa gafara kuma ko ba ka yafe masa ba Allah zai yafe masa, duk da Legit Hausa ba ta da tabbacin ta fadi haka.
A cewarsa:
"Manzon Allah SAW ya ce duk wanda ya ce a yafe masa aka ki yafe masa Allah zai yafe masa kai kuma da ba ka yafe shi ba kai da Allah."
Daga baya an ji cewa malamai sun nuna rashin ingancin wannan hadisi har ta kai wasu sun yi wa Sheikh Triumph raddi saboda kafa hujja da shi.

Source: Facebook
2.. Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa na daya daga cikin malaman da suka fara magana bayan rasuwar Muhammdu Buhari.
Sheikh Daurawa ya roki ƴan Najeriya su sanya Muhammadu Buhari a addu'o'insu kuma su yafe masa kura-kuransa.
Babban kwamandan rundunar Hisbah ta Kano ya yi wannan roko ne yayin da ake jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasar a Najeriya.
Malamin ya kuma roƙi jama'a su yiwa tsohon shugaban ƙasar addu'ar samun rahama a wurin Allah bayan rasuwarsa a birnin Landan.

Source: Facebook
3. Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah
Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya tayar da kura a kafofin sadarwa bayan ya yi magana game da yafewa Buhari a Najeriya wanda ya wallafa a Facebook.
Malamin ya ce ko da ba a yafewa Buhari ba Allah na iya yafe masa a cikin rahamarsa wanda wannan bayani ya jawo maganganu.
Ya ce:
"Maganar da wasu ke fada a ji ta daga baki na wai cewa idan hakki na Allah ne zai yafe, na bayi kuma sai idan bayi sun yafe, wannan maganar banza ce ba gaskiya ba ce.
"Ba Allah ba ne ya fada kuma ba manzon Allah SAW ba ne ya fada, idan haka ne ashe bai zama Allah ba kenan."

Source: Facebook
4. Sheikh Ishaq Adam Ishaq
Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yi jawabi mai ratsa zuciya kan rasuwar Muhammadu Buhari, inda ya bukaci shugabanni su ji tsoron Allah.
Ya soki malamai da ke cewa Allah SWT zai yafe wa Buhari duk da wasu ba su yafe masa ba, yana cewa hakan kuskure ne babba.
Baristan ya bayyana cewa Allah ba zai yafe hakkin wani mutum ba sai wanda aka zalunta ya yafe ko kuma an biya shi hakkinsa.
Martanin nasa na zuwa ne bayan Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya fitar da bidiyo kan yafewa Buhari.

Source: Facebook
5. Sheikh Bello Aliyu Yabo
Sheikh Bello Aliyu Yabo ya yi magana game ce-ce-ku-ce da ake ta yi bayan rasuwar marigayi Muhammadu Buhari kan yafe masa.
A cikin bidiyon, Bello Yabo ya ce ta yaya wasu malamai za su yi amfani da hadisi cewa ko ba ka yafe ba Allah zai tafe masa.
Malamin ya ce abin takaici ne kana ganin wadanda suka kwashe muku dukiya suna facaka amma ace a yafe musu.
Ya bayyana cewa su kam ba su yafe ba saboda bai cika sharudan tuba ba kafin ya bar duniya kuma sai an biya shi hakkinsa a lahira.

Source: Facebook
Sheikh Pantami ya tuna alherin Buhari gare shi
Mun ba ku labarin cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya ce ya zauna da Muhammadu Buhari na tsawon shekaru 24 kuma bai taba ganin rashin gaskiya a tare da shi ba.
Pantami ya bayyana cewa Buhari mutum ne mai gaskiya, kishin kasa da jajircewa, yana tunawa da kyawawan halayensa da sadaukarwa ga jama'a.
Ya ce maganar cewa Buhari bai kyauta ba gaskiya ba ne, ya sha samun kyaututtuka daga gare shi har guda biyu da ba zai manta ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



