Jigon APC Ya Yi Fatali da Tsarin Jam'iyya Mai Mulki, Ya Yi Barazanar Sauya Sheƙa
- Tsohon ɗan takarar shugabancin APC na kasa, Sunny Moniedafe ya ce jam’iyyar na cikin barazanar ruguje wa baki ɗaya
- A tsokacin da ya yi kan ƙalubalen da APC ke fuskanta, ya ce abin mamaki ne yadda ake da sassan daban-daban a jam'iyya
- Ya fadi yadda shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya gaza da tare da yin barazanar shi ma zai iya fice wa daga cikinta idan na a gyara ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban APC na ƙasa, Sunny Moniedafe, ya bayyana rashin gamsuwa da yadda Shugaba Bola Tinubu ke tafiyar da mulki.
Jigon ya kuma yi zargin cewa sakon yadda Shugaba Tinubu ke jan ragamar jam'iyyar zai jefa ta a sarƙaƙiya mai wahalar warware wa.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Channels TV, inda ya nuna damuwa cewa jam’iyya mai mulki na iya fuskantar rugujewa nan gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon APC ya magantu kan tsagin ANPP
Daily Post, Moniedafe ya yi tsokaci kan bukatun wasu tsofaffin ƴan ANPP, waɗanda suka bukaci cewa kujerar mataimakin shugaban ƙasa ta ci gaba da kasancewa a hannunsu.
Sai dai ya soki ci gaba da dogaro da tsagin tsofaffin jam’iyyun da suka haɗu da APC – wato ANPP, CPC da ACN – yana mai cewa hakan na kara rarraba kawunan ‘ya’yan jam’iyyar.
Ya ce:
“Ya kamata mu daina wadannan tsofaffin rigingimun. Lokacin da CPC ta fito da nasu tsagin, na nemi mutane da dama domin a tunatar da shugaban ƙasa cewa ACN ma tana nan tafe "
Ya yi barazanar cewa idan al'amura suka ci gaba da tafiya a halin da ake ciki yanzu, zai tattara ya fice daga jam'iyya mai mulki.
Ƙusa a APC ya caccaki jagorancin Tinubu
A cikin tattaunawar, Moniedafe ya fito fili ya soki shugabancin salon jagorancin Bola Tinubu da ya ke ganin zai iya kassara APC.
A cewarsa:
“Ina ganin muna cikin haɗari. Kuma ina bakin ciki in ce haka – Shugaba Tinubu ba ya abin da ya kamata.”
Ya kara da cewa ya kamata manyan jam’iyyar su rika kare manufofin gwamnati, amma da yawa daga cikinsu ko dai suna shiru ko kuma ba su san abin da za su ce ba.

Source: Facebook
Moniedafe ya ce kamata ya yi shugaban ƙasa ya gayyato dattawan jam’iyyar domin su zauna a kan batun APC.
Jigon ya kuma soki matakin cire tallafin mai da kuma kalaman Shugaba Tinubu yayin da yake zaben Mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima.
A cewarsa:
“Ban taɓa jin wani yana neman wa’adi na biyu tun daga rana ta farko da aka rantsar da shi ba."
Onanugu ya kare kyautar Tinubu ga Falcons

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC
A baya, kun ji cewa Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fito ya kare kyaututtuka da kuɗin da Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ‘yan wasan Super Falcons.
Kowace ‘yar wasa daga cikin tawagar ta samu lambar yabo ta kuɗi da ta kai N150m, yayin da kowane ɗan na kwamitin horaswa ya samu Naira miliyan 75.
Wasu daga cikin ‘yan Najeriya na ganin cewa kyautar da Tinubu ya bayar ta yi yawa, ganin cewa wasu daga cikin ma'aikatan ƙasar nan na cikin matsin albashi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

