Sauki Ya Samu: 'Yan Kasuwa Sun Dawo da Farashin Fetur Kasa da na Dangote, NNPCL

Sauki Ya Samu: 'Yan Kasuwa Sun Dawo da Farashin Fetur Kasa da na Dangote, NNPCL

  • Rahotanni sun nuna cewa 'yan kasuwa a Najeriya sun fara saida fetur da kasa da farashin da Matatar Dangote ke bayarwa
  • Bayanai sun nuna cewa masu shigo da man fetur sun ce sun rage farashin ne don a cigaba da damawa da su a kasuwar mai
  • Hakan na zuwa ne bayan Aliko Dangote ya bukaci gwamnati ta haramta shigo da fetur daga waje domin karfafa masana’antun gida

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A wani mataki da ke kara zafafa gasa a bangaren man fetur a Najeriya, wasu 'yan kasuwa da ke shigo da fetur daga waje sun fara saida shi da farashi kasa da na matatar Dangote.

Wannan na zuwa ne yayin da Alhaji Aliko Dangote ke kira ga gwamnatin tarayya da ta haramta shigo da fetur domin karfafa harkar tace danyen mai a gida.

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Farida Sultana da wasu mata 'yan Arewa 2 sun shiga shirin BBNaija

Ma'aikaci na sayar da man fetur a Najeriya
Ma'aikaci na sayar da man fetur a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar Punch ta yi wani rahoto kan yadda 'yan kasuwa suka rage farashin da dalilin daukar matakin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan kasuwa sun rage farashin man fetur

Rahotanni daga jihohin Lagos da Ogun sun tabbatar da cewa wasu gidajen mai na saida fetur din ne a tsakanin N847 da N860.

A daya bangaren kuma, abokan hulɗar Dangote irin su MRS da Heyden ke sayarwa tsakanin N865 da N875.

An gano cewa wasu masu rarraba mai daga wuraren ajiya suna saida fetur din ne da kasa da N820, wanda shine farashin da Dangote ke sayar da lita guda.

Wasu kamfanoni irin su Aiteo da Menj na saida da litar mai a N815, wanda ke nuna cewa farashi yana sauka sosai.

Dalilin sauke farashin mai a Najeriya

Masu rarraba mai sun tabbatar da cewa sun rage farashi saboda har yanzu suna fama da rashin riba, musamman tun bayan da matatar Dangote ta fara rage farashinta a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Ana zaman ƙeƙe da ƙeƙe tsakanin 'yan Arewa da jami'an gwamnatin Tinubu a Kaduna

Wannan gasa ta kara sa wasu su fara kokarin janyo kwastomomi da farashi mai rahusa domin kaucewa yin kwantai.

IPMAN ta bayyana ra’ayinta kan lamarin

Sakataren yada labarai na kungiyar 'yan kasuwan man fetur masu zaman kansu (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya tabbatar da cewa wasu na rage farashi.

Ya ce wasu na rage farashin fetur zuwa N815 da N817, yayin da Dangote ke nan da N820, sai kuma NNPCL da ke sayar da shi a N825.

A cewarsa, wannan wani bangare ne na kyakkyawan sakamako da aka fara samu bayan barin kasuwa ta yi halinta.

Alhaji Aliko Dangote da ya mallaki matatar mai
Alhaji Aliko Dangote da ya mallaki matatar mai. Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Maganar hana shigo da man fetur

Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa cigaba da shigo da man fetur daga kasashen waje yana hana masana’antun cikin gida cigaba da aiki yadda ya kamata.

Vanguard ta wallafa cewa ya ce hakan yana sanya 'yan kasuwa cikin gida su rasa kwarin gwiwar saka jari a fannin tace mai.

Sai dai 'yan kasuwa sun nuna kin amincewa da hakan tare da kira ga shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da bukatar.

Kara karanta wannan

Jirgin ƙasa dauke da fasinjoji 100 ya yi hatsari yana cikin gudu, an rasa rayuka

Shettima ya magantu kan tallafin mai

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya yi magana kan cire tallafin man fetur.

Kashim Shettima ya ce abubuwa da dama da suka shafi tattalin arziki ne suka sanya Bola Tinubu daukar matakin.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne yayin da wasu 'yan kasuwa suka kai masa ziyara a fadar Aso Rock Villa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng